𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Don Allah meye hukuncin wanda idan yaga anyi kuskure yake tozarta mutum a cikin jama'a? Shugaba ne na makaranta yake jan jam'i, rana ɗaya ɗalibi ya ja, da aka idar da Sallah sai aka fara yiwa ɗalibin tozarta a gaban ɗalibai maza da mata, kan cewa bai kamata ba, ni ina ganin da an kira shi gefe an masa faɗa da ƙarin haske ko a haɗa su iya maza ayi musu zai fi, mene ne hukuncin haka?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikum assalam. Yiwa mutum Nasiha a cikin mutane bai
dace ba, kuma hanya ce da zata hana shi amsar nasihar, in ba wanda aka yiwa
nasihar yana da tsananin ikhlasi ba. Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) Yana
cewa: "Wanda ya suturta Musulmi Allah zai suturta shi", kamar yadda
Muslim ya rawaito a Hadisi mai lamba (2074).
Allah ne mafi sani.
Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.