Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Zan Iya Haduwa Da Mijina Na Farko A Aljanna

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam matar da mijinta ya mutu, sai ta yi wani auren, shin za ta sake haɗuwa da na farkon a lahira, in dukkansu sun shiga aljanna, ko kuma na karshen shi ne zai zama mijinta a can?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

To yar'uwa malamai sun yi saɓani akan wannan mas'alar zuwa zantuttuka guda uku

1. Zata zauna da wanda ya fi kyawawan dabi'u a duniya.

2. Za a ba ta zaɓi.

3. Za ta zauna da na karshensu.

Wannan maganar ta karshe ita ce mafi inganci saboda Faɗin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa: "Duk matar da mijinta ya mutu, ta yi aure a bayansa, to ranar lahira za ta kasance ga na karshensu" Albani ya inganta shi a Sahihu-jamiussagir a hadisi mai lamba ta : 2704.

Wannan kuma shi ne dalilin da ya hana matar Abuddarda'a aure bayan mijinta ya mutu, lokacin da Mu'awiya ya nemi ya aure ta, ta ki yarda ta aure shi, saboda tana so ta zauna da abudarda'a a lahira. duba silsilasahiha hadisi mai lamba ta : 1281

Munawy yana cewa: "Malamai suna cewa: Wannan shi ne ɗaya daga cikin dalilan da suka sa matayan Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ba su yi aure ba bayansa, saboda Allah ya riga ya kaddara cewa matayansa ne a aljanna" duba Faidhul-kadeer 3\151

Allah ne mafi sani.

Dr Jameel Zarewa

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments