Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene Ne Hukuncin Mahaifi Ya Dinga Ba Da Kyauta Ga Dan Da Ya Fi Yi Masa Biyayya

TAMBAYA (119)

Slm. Malam Barka da warhaka Allah y Kara lafiya. Malam nasha yin tambaya ba'a amsawa amma bazan gaji ba watarana za'a amsa. Malam don Allah meye hukuncin kyautar da uba yayiwa mutum daya acikin yayansa saboda yafiyimasa biyayya akan sauran yaya shin ya halatta ka bawa wanda yafimaka biyayya kyautar wani abu ka hana sauran ya'yan kuma shi wanda aka bawa kyautar yana rikewa mahaifin gurin sana'ar sa wacce ake hidima da kudin a gida.meye hukuncin wannan kyautar

AMSA

Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuh

✍️AMSA A TAQAICE

(Ya zama dole ya kyautata musu ba tare da nuna banbanci ba. Amman idan sun hada baki akan a bawa daya daga cikinsu wani abu su kuma su hakura to suna da damar yin hakan, ba laifi bane ba)

Bismillaahir Rahmaanir Raheem

An yiwa Shaykh Saleh al-Munajjid (Hafizahullah) tambaya makamanciyar wannan tambayar. Ya ce

Ba shakka wasu yayan sun zarce wasu, wannan abu ne sananne. Saidai shi mahaifin ba shi da zabin ya fifita wani akan wani. Sabanin haka, saidai ya dauke su a matsayi daya kamar yanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Ku ji tsoron Allah sannan ku mu'amalanci yayan ku ba tare da nuna musu fifiko ba"

Don haka bai halatta mahaifin nasu ya fifita son daya akan daya ba saboda daya yafi daya kyautatawa iyayen ba. Ya kamata ya mu'amalance su daidai kuma ya yi adalci a tsakaninsu ta yanda zasu girmama shi kuma su bi umarnin Allah da ManzonSa. Kada ya bayyana son daya akan daya ta hanyar bawa daya kyauta ya hana daya

Dukkansu darajarsu daya ce a bangaren gado da kuma kyauta kamar yanda Shari'ar musulunci ta tabbatar ta yanda za'a bawa namiji kaso daya da za'a bawa mata biyu. Idan ya bawa daya daga cikin yayansa kyautar 1,000, yar sa kuma zai bata 500. Amman idan yayan nasa sun kasance wayayyu masu ilimi da haquri, sai suka taru suka ce ka bawa dan uwanmu kaza da kaza, ba tare da sun damu ba, kamar su ce ka bashi mota ko kuma gida ko kudade ba tare da sunyi hakan saboda tsoro ko kunya ba to wannan ba matsala, ya halatta

Muhallish shahid anan shine; ya zama dole ya kyautata musu ba tare da nuna banbanci ba. Amman idan sun hada baki akan a bawa daya daga cikinsu wani abu su kuma su hakura to suna da damar yin hakan, ba laifi bane ba

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa

Shaykh Saleh al-Munajjid (Hafizahullah)

Compiled

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments