TAMBAYA (106)❓
Mene ne hukuncin macen da take saka hoton ta a Facebook page, musamman matan da suke cewa dora hotunansa sanye da hijabi ba haramun bane a Shari'ah? Zaku iya min bayani ta yanda ni kuma zan basu shawara akan hakan?
AMSA❗
Alhamdulillah
Haramun ne mace ta dora hoton ta a Facebook ko kuma wata
kafar sadar zumunta saboda dalilai kamar haka;
Dorawar sanye da hijabi ya ci karo da abinda ya bayyana daga
cikin Qur'ani da Sunnah. Allah (Subhanahu wata'ala) yace, dangane da mata
nagari wadanda sun nesanta daga dukkan zargi, sune matayen Annabi (Sallallahu
alaihi wasallam):
وَإِذَا
سَأَلْتُمُوهُنَّ مَتَاعًا فَاسْأَلُوهُنَّ مِن وَرَاءِ حِجَابٍ ۚ ذَٰلِكُمْ أَطْهَرُ
لِقُلُوبِكُمْ وَقُلُوبِهِنَّ ۚ
الأحزاب
(53) Al-Ahzaab
"Kuma idan zã ku tambaye su waɗansu kãyã, to, ku tambaye su daga bãyan
shãmaki. Wannan ya fi muku tsarki ga zukãtanku da zukãtansu"
(يَا أَيُّهَا
النَّبِيُّ قُل لِّأَزْوَاجِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَاءِ الْمُؤْمِنِينَ يُدْنِينَ عَلَيْهِنَّ
مِن جَلَابِيبِهِنَّ ۚ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَن يُعْرَفْنَ فَلَا يُؤْذَيْنَ ۗ وَكَانَ
اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا)
الأحزاب
(59) Al-Ahzaab
"Yã kai Annabi! Ka ce wa mãtan aurenka da 'yã'yanka da
mãtan mũminai su kusantar da ƙasã
daga manyan tufãfin da
ke a kansu. Wancan ya fi sauƙi ga a gane su dõmin kada a cũce
su. Kuma Allah Yã
kasance Mai gãfara,
Mai Jin ƙai"
Sannan kuma Allah yayi hani da mata su dinga magana mai
sanyi, kamar yanda Ya fada:
(يَا نِسَاءَ
النَّبِيِّ لَسْتُنَّ كَأَحَدٍ مِّنَ النِّسَاءِ ۚ إِنِ اتَّقَيْتُنَّ فَلَا تَخْضَعْنَ
بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي فِي قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلًا مَّعْرُوفًا)
الأحزاب
(32) Al-Ahzaab
"Yã mãtan Annabĩ! Ba ku zama kamar kõwa ba daga mãtã,
idan kun yi taƙawa, sabõda
haka, kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cũta a cikin zuciyarsa ya yi ɗammani, kuma ku faɗi magana ta alheri"
Allah (Subhanahu wata'ala) ya umarci matan Annabi
(Sallallahu alaihi wasallam) da sauran mata muminai baki daya, su dinga saka
hijabi, domin su tsarkake zuciyarsu da kuma kare su daga duk wani abinda ka iya
janyo musu sanadin fitina ko zargi, saboda kiyaye mutuncinsu da kuma na sauran
mata muminai
Idan aka fahimci haka, to za'a gane cewar duk macen da ta
dora hoton ta a kafafen sada zumunta, ta yanda nagari da tanbadaddu zasu gani,
kai tsaye yin hakan ya ci karo da abinda Allah (Subhanahu wata'ala) ya koyar
Yin hakan yana bude kofar barna (fitina) sannan kuma sharri
ne ga wadda ta dora da kuma wadanda suka kalla. Sau nawa muna karanta tare da
jin labaran illar dora hotuna a kafafan sada zumunta? Adadin mata nagari nawa
ne suka taba fadawa tarkon wadanda basa tsoron Allah, gurbatattun mutanen da
suke rudarsu da magana mai dadi da kuma alqawarirrika har sai lokacin suka
cimma muradinsu su juya musu baya su kyale su da yin da na sani, kunya anan duniyar
da kuma a lahira (Allah ya kiyaye)
Masu barna nawa ne suke ruduwa da irin wadannan hotunan har
ma su canza su ta hanyar saka hoton fuskar mutuniyar kirki akan hoton jikin
mace tanbadaddiya, silar hakan tayi nadama, ta jazawa iyayenta nadama a ranar
da da na sani zata zama keya
Dangane da matan da kika ce sun ce ba haramun bane saka hoto
da hijabi a kafar sada zumunta, idan kina nufin hijabin da Shari'ah ta ce a
saka, idan fuskar ta ba ta bayyana ba, tabbas wannan ba haramun bane ba a
musulunci, musamman idan an buqaci hakan. To amman ba haka suke nufi ba, domin
kuwa babu wata fa'ida a yin hakan. Mene ne amfanin dora bakin hoton da ba
abinda ya fito?
Abin nufi shine, saka hoton mace fuskarta a bude ko da ace
ta rufe gaba daya jikinta, munyi bayanin illar sa ta yanda yin hakan ya wadatu
ya janyo haramci, ko da kuwa ba mu ce ya halatta mace ta rufe fuskar ta ba, ina
kuma ga idan wajibi ne yin hakan? Zunubin zai ribanyu hatsarin kuma zai
girmama. Idan tayi hakan ta ketare iyaka kuma ta bijirewa abinda aka umarci
mata suyi zamunna dayawa
Al-Ghazali (Rahimahullah), a cikin littafinsa: Ihya 'Ulum
ad-Din (2/53) ya ce: "Shekaru aru aru, mazaje fuskarsu a rufe take yayin
da su kuma mataye fuskarsu take a rufe". An rawaito irin wannan a cikin
Fath al-Bari, (9/337)
Al-Hafiz Ibn Hajar al-Asqalani (Rahimahullah), a cikin Fath
al-Bari (9/424), ya ce: "Al'adun mata a da can da kuma yanzu shine suna
rufe fuskokinsu a gaban wadanda ba maharramansu ba"
Dadin dadawa, idan mutum mai hankali ya gano cewar
kyakkyawan wajen da yake daukar ido da kuma janyo fitina a jikin mata shine
fuska, kuma shine abinda maza suke son kalla, kuma ta hakan ne za'a iya gane
mace kyakkyawa ce ko mummuna, to bayyana hoton ta kamar yanda bayani ya gabata
zai bude kofar barna ga wannan macen, kuma komai zai iya biyo baya sakamakon
dora wannan hoto a kafafen sada zumuta (media platforms)
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa:
Shaykh Muhammad Saalih al-Munajjid (Hafizahullah)
Fassarawa:
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.