Ticker

6/recent/ticker-posts

Addu'ar Yafe Zunubbai Ko Da Sun Zarce Yawan Kumfar Teku

TAMBAYA (116)

Assalamu alaikum. Allah y taimiki malam addu ar yafe zunibai

AMSA

Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuhu

✍️AMSA A TAQAICE

(Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Babu wani bawa da zai aikata wani zunubi, sannan ya kyautata alwala, ya tashi ya yi sallah raka'a biyu, sannan ya nemi gafarar Allah, face Allah ya gafarta masa)

Bismillaahir Rahmaanir Raheem

To dan uwa, Sayyadil Istighfari ya kamata ka yi domin kuwa Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: Duk wanda ya karanta;

"Allahumma anta rabbi la'ilaha illa anta, khalaqtani wa'ana abduka, wa'ana ala ahdika, wa'ahdika masta'da'atu, abu'ulaka bini'imatika alayya, wa'abu'u laka bi zanbi faghfirli, fa'innahu la yaghfiruz zunuba illa anta"

Da safe da kuma yamma, to Allah (Subhanahu wata'ala) zai yafe masa zunubban sa komai yawan su

(Sahih Hadith)

Haka kuma a cikin littafin Hisunul Muslim da akwai addu'o'i akan Abin Da Wanda Ya Aikata Wani Zunubi Zai yi kuma Ya Fada

Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Babu wani bawa da zai aikata wani zunubi, sannan ya kyautata alwala, ya tashi ya yi sallah raka'a biyu, sannan ya nemi gafarar Allah, face Allah ya gafarta masa.

Sannan kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Na rantse da Allah! Ina neman gafarar Allah, kuma ina tuba zuwa gare shi, a kowace rana sama da sau saba'in.

(Bukhari da Muslim)

Kuma ya ce, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, "Ya ku mutane! Ku tuba zuwa ga Allah. Domin ni ina tuba a kowace rana zuwa gare shi sau dari.

Kuma ya ce, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, "wanda ya ce;

أَسْتَغْفِرُ اللهَ الَّذِي لاَ إِلَهَ إلاَّ هُوَ الْحَيُّ القَيّوُمُ وأَتُوبُ إِلَيهِ.

Astaghfirul-lahal-lazee la ilaha illa huwal-hayyul-qayyoomu wa-atoobu ilayh.

Ina neman gafarar Allah, Allah babu abin bautawa da gaskiya sai shi, rayayye, Mai tsayuwa da komai, kuma ina tuba zuwa gare shi.

Allah zai gafarta masa zunubansa ko da zunubin guduwa daga fagen fama ne".

Kuma ya ce, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, "Mafi kusancin da Allah yake kasancewa da bawansa a tsakiyar karshen dare ne. Don haka idan kana da ikon kasancewa cikin masu ambaton Allah a wannan lokacin to ka kasance".

Kuma ya ce, tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi, "mafin kusancin da bawa yake kasancewa da Ubangijinsa yayin da yake sujada ne, don haka ku yawaita addu'a (a cikin sujada)".

Kuma manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Hakika a kan lullube zuciyata, kuma ni ina neman gafarar Allah sau dari a rana".

Don haka yakai dan uwa, ina fatan daga ni har kai Allah ya jikanmu, mu dage mu yawaita Istighfari domin kuwa har yanzu rana bata fito daga yamma ba ballantana ace kofar tuba ta rufe

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments