Ticker

6/recent/ticker-posts

Tasirin Zamananci A Kan Camfe- Camfen Hausawa

TASIRIN ZAMANANCI A KAN CAMFE- CAMFEN HAUSAWA

Na

Aminu Musa

07036420021

ameenumusa12@gmail.com

BINCIKEN DA AKA GABATAR DOMIN CIKA KA'IDA TA SAMUN TAKARDAR SHAIDAR MALANTA TA KASA (NCE) A SASHEN NAZARIN HARSHEN HAUSA KWALEJIN ILIMI TA ISA KAITA DAKE DUTSINMA.

 OGASTA 2008

 SHAFIN AMINCEWA

1. Sa Hannun Mai Duba Aiki..................

Kwanan wata..................................

2. Sa Hannun Shugaba Sashe............,...

Kwanan wata..................................

3. Sa hannu Shugaban Makaranta........

Kwanan wata..................................

 GABATARWA

Da farko a cikin babi na daya wannan bincike ya yi magana a kan filin bincike da manufar bincike da muhimmancin bincike da Dalilin bincike na wannan aiki.

Sannan kuma a babi na biyu an yi magana ne akan Ma'anar Tasiri da Ma'anar Zamananci da nuna su wanene Hausawa da Ma'anar canfe-canfen Hausawa da ire-iren camfe-camfe Hausawa da bitar Ayyukan da suka gabata.

A cikin babi na uku an yi bayanin hanyoyin tattara bayanai da matakan gudanar da bincike da tasirin gudanar da bincike. Haka kuma a babi na hudu an yi bayanin tsarin Zamananci ga al'ummar Hausawa da matsayin canfe-canfe a al'ummar Hausawa jiya da yau da tasirin Zamananci akan canfe-canfen Hausawa da muhimmancin canfe-canfe da illolinsa. Bugu da Kari babi na biyar shi ne na karshe a cikinsa akwai shawarwari da kuma takaitawa da kammalawa. Haka kuma a karshe ya bayyana ire-iren Manazarta wato inda aka samo cikakken bayanai.

 SADAUKARWA

Na Sadaukar da wannan kundin bincike nawa kacokan ga Mahaifina Marigayi Musa Ibrahim Dansarai da Allah yayi wa rasuwa. Haka kuma sadaukarwa ne ga mahaifiyata da 'yan uwa na maza da mata da iyalaina da sauran zuriyar Musulmi baki daya.

 GODIYA

Ina mika godiya ga Allah Madaukakin sarki da ya raya ni cikin ikonsa kuma ya bani damar shiga makaranta cikin nasara tun daga firamare har zuwa wannan mataki na NCE Allah ya kara tsira da Aminci ga fiyayyen halitta cikamakin Annabawa.

Sannan ina mika Godiya ta musamman ga Mahaifana da yan uwa da abokan arziki. Ba zan manta da gudummuwar abokin mahaifina ba Inspector Musa Amadu da iyalansa da danginsa baki daya. Ina godiya ga Goggo Asma'u da mijinta da yayanta baki daya Allah ya saka masu da alheri Amin.

Ina God ga abokaina na gida Dana makaranta Daga karshe ina mai salati ga fiyayyen halittu Annabi Muhammadu SAW

Shafin Amincewa ...... ........ ...... .... I

Shafin Gabatarwa............................... .........II

Shafin Sadaukarwa.. ............................ .......III

1.0 Babi Na Daya................................. ........1

1.1 Filin Bincike..................... .......................1

1.2 Manufar Bincike............ .........................1

1.3 Dalilin Bincike.......................... ...............2

2.0 Babi Na Biyu.............................. .............2

2.1 Bitar Ayyukan Magabata........ ...............3

2.2 Tasiri.............................. .........................4

2.3 Zamananci.......................... ...................5

2.4 Su wa Nene Hausawa............. .............7

2.4.1Ra'ayin Malaman Tarihi.......... ...........9

2.4.2 Ra'ayin Jostha...................................10

2.4.3 Ra'ayin S.G Smith..............................12

2.4.4 Ra'ayin Mahadi Adamu.....................14

3.0 Babi Na Uku...........................................16

3.1 Hanyoyin Gudanar Da Bincike..............18

3.2 Matakan Gudanar Da Bincike...............20

3.3 Tasirin Gudanar Da Bincike..................24

4.0 Babi Na Hudu.........................................30

4.1 Tasirin Zamananci Ga Hausawa........24

4.1.1 Ta Fuskar Al'ada...............................26

4.1.2 Ta Fuskar Tarbiyya...........................27

4.1.3 Ta Fuskar Kiwon Lafiya....................30

4.1.4 Ta Fuskar Kasuwanci........................32

4.2 Canfi Kafin Musulunci..........................37

4.3 Canfi Bayan Zuwan musulunci............44

4.4 Tasirin Zamananci akan canfe-canfen Hausawa..51

4.5 Muhimmancin canfe-canfe..................56

4.5.1 Koyar Da Tarbiyya..............................57

4.5.2 Inganta Kiwon Lafiya.........................59

4.5.3 Kaifafa Tunani....................................60

4.5.4 Kyautata Tarihi...................................68

4.5.5 Adana Al'ada......................................71

4.5.6 Gyara Zamantakewa.........................77

4.5.7 Inganta Imani.....................................82

5.0 Babi Na Biyar.........................................85

5.1 Takaitawa..............................................87

5.2 Kammalawa..........................................89

5.3 Shawarwari...........................................91

Manazarta

 BABI NA DAYA

 Gabatarwa

1.1 FILIN BINCIKE

Wannan bincike namu zai yi tsokaci ne a kan Canfe-Canfen Hausawa. Sa'annan kuma, wannan bincike zai fito mana da rawar da canfi yake takawa a rayuwar Hausawa. Haka kuma, binciken zai fara shiga ciki domin ya zakula mana ma'anar Canfi da ire-iren canfi. Bugu da kari, wannan bincike zai fiddo ma'ana da gudumuwar cla Canfe-Canfen suka bayar ga al'ummar Hausawa. Daga karshe wannan bincike zai bayyana mana irin tasirin Zammanci a kan Canfe-Canfen Hausawa.

1.2 MANUFAR BINCIKE

Manufar wannan bincike zai yi kokarin fito mana da ma'anar Canfi da kuma ire-irensa ga al'ummar Hausawa..

Haka kuma, binciken zai fadakar da dalibai masu nazarin harshen Hausa a manyan makarantu harma da dalibai da ke a sakandare masu sha'awar nazarin harshen Hausa ko karanta Hausa. Bugu da kari binciken zai zama hanyar ilimantar da al'ummar Hausawa, musamman masu nazarin harshen Hausa a manyan makarantu da muke da su. Daga karshe Canfi yana da muhimmanci kwarai da gaske ga masu nazari a manyan makarantun kasar nan, da sauran dalibai masu sha'awar yin nazari a wasu wurare da ba a yi na zari a kan su ba. Bincike da kara gogewa a fagen nazarı.

Binciken kuma, yana da muhimmanci ga makarantu musamnman a sashen nazarin harshen Hausa. Saboda ganin irin yadda sashen nazarın harshen Hausa yake, saboda samar da kundayen bincike a yawancin makarantu.

Bugu da kari, wanna nazari zai karawa masu bincike kwarin guiwar yadda za su kara, wa gudummuwar su ta bangaren cigaban harshen hausa ga al'urnmar hausawa baki daya. A takaice dai wannan bincike namu yana da muhimmancin kwarai da gaske dangane da yadda a kullum, musamman dangane da abubuwan da suka shafi rayuwarsu da kuma lafiyarsu gaba daya.

1.3 DALILAN BINCIKE

Sha'awar mu da wannan bincike bata wuce gurinmu na mu gano ma'anar canfi da ire-irensa da kuma matsayin sa a al'ummar Hausawa ba. Haka kuma ana gudunar da bincike don gano sabon abu ko ilimi ko karin bayani ko Karin haske ko ci gaba a kan abin da wani ya aiwatar da nufin ilimantar da al'umma baki daya a cikin hanya mafi saukin fahimta. Haka kuma, dalilin wannan bincike namu shi ne ganin yadda al'ummar Hausawa take kara lalacewa, muka ga ya dace da mu yi tsokaci akai don kawai mu samar da gyara a rayuwar al'ummar hausawa ta hanyar nuni wajen cusa kyawawan halaye da dabi'u masu ladabtarwa ga al'ummar.

Bugu da kari, muna masu yin alfahari da wannan bincike namu ta hanyar da zai zame mana abin dogaro ko ya zame ma 'yan baya abin dubawa ko Karin haske ga binciken da suka sa agaba

2.0 BABI NA BIYU

2.1 BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

Hakika ayyuka da dama sun gabata dan gane da Canfe-Canfen al'ummar Hausawa a shekarar (1977) wani masani mai suna M. B. Umar ya kawo Ma'anar Canfe-Canfen da ire-irensa. Haka kuma, yayi yunkurin fito da muhimmancinsa da illolinsa.

Sai kuma a shekarar (1982) wani masani maisuna M.S Ibrahim A cikin bayaninsa na dangantakar al'ada da addini ya fito da ta hakikanin ma'anar canfe canfe da rabe-raben sa ga al'ummar hausawa.

A shekarar (1984) Dr. A. Dan-Gambo. Ya gabatar da wani kundun bincike na rabe reben adabin hausawa da muhimmancinsa ga raywar hausawa a sashen harsunan jami'ar Bayero da ke kano. A cikin wannan aikin yayi kokarin fitowa jama'a ma'anar camfe-camfe da ire-rensu.

Haka kuma, Malam Sani Mu'azu jingir, (1982) a cikin littafinsa mai suna zaman Hausawa da al 'adunsu ya fito da ma'anar canfe-canfe da kuma ire-irensu da muhimmanci su da illolin sa ga al'ummar Hausawa.

Shi ma, Usman Ussaini Fagge, (1998) ya bayyana su wa wanene Hausawa a cikin ireiren tsarin harshen Hausa na rukuni.

Aliyu Mohammed Bunza (2006) a littafinsa mai suna Gadon fede al 'ada ya kawo abubuwa da dama dangane da canfe-canfen hausawa. Domin kuwa a cikin littafin ne ya bayyana tarihin samuwar Canfi ga al'ummar Hausawa, sa'annan kuma, ya karkasa canfi gida-gida dangane da al'ada ya ci gaba da fito da ire-iren canfe-canfe da muhimmancinsa ga al'ummar Hausawa.

Haka kuma, farfesa Mahadi Adamu, (1991) A cikın littafinsa mai suna the Hausa factor in west African history shi ma ya fito da ma 'anar Canfe-Canfen Hausawa da ire-iren sa da illolinsa. Sannan kuma, (2005) Mukalar Malam Tukur Lawal Sha'iskawa mai taken al'adun Hausawa ya bayyana ma'anar Hausawa tare da al'adunsu. Sannan kuma, ya fitar da ma'anar Canfe-Canfe ga al'ummar Hausawa tare da kaworabe-rabensa. Rubuce-rubuce a kan canfi bai tsaya ga nan ba akwai Jami'ar Bayero da ke kano (1982) sun bayyana ma'anar Canfe-Canfen Hausawa. sannan sun kawo ire irensu. Haka kuma, sunyi kokarin zakulo muhimmancin sa tare da kawo illolinsa ga al'ummar Hausawa. Dakta Bashir Safana Janmi'ar Katsina, (Katsina state university) a wata tattaunawa da muka yi da shi a gidansa da ke Safana, ya bayyana mana ma'anar tasiri da kuma zamanci.

Idan aka dubi irin wadannan aikace-aikace da suka gabata dangane da Canfe-Canfe za a ga cewa har yanzu akwai, bukatar a kara ci gaba da samar da littatafai da kuma kundayen binciken a kan Canfe-Canfe da za'a iya samu dangane da matsayin Canfi a al'ummar Hausawa.

2.2 TASIRI

Tasiri, a taikace wannan kalma ta tasiri tana daya daga cikin jerin fitatun kalmomin da Hauswa suka kebe domin bayyana matsayin ko rawa ko kima ta wani abu. Tasiri na nufin irin rawar da wani abu ya taka a kan wani abu. Wato manufa a nan dukkan wani canji ya alla mai kyau ko marar kyau da wani abu ya samu. A takaice tasiri na nufin ci gaba ko koma baya da wani abu ya samu bisa wasu dalilai ya alla na boye ko na sarari.

2.3 ZAMANCI

Zamanci yana nufin yanayi ko halin da al'unmma suka tsinci kansu a ciki sakamakon shudewa ko wucewa na wani mulki ko shugabanci da wani ya taba yi, atakaice zamani ya kanzo lokaci -lokaci Haka kuma, zanananci yana nufin dukkan canji da aka samu daga tsohuwar al'ada ta gargajiya wadda aka gada daga kaka-da-kakanni. Atakaice za a iya kallon zamananci a matsayin tasiri da zamani ya haifar ko canje-canjen da zamani ya samar ga al'adun Hausawa na gargajiya ko a kan rayuwar al'ummar Hausawa baki daya.

2.4 SU WANE NE HAUSAWA?

Usman Usaini Fage (1982) A cikin littafinsa mai suna ire-iren Karin harshen hausa na rukuni ya bayyana Hausawa da cewa. Magana a kan su wanene Hausawa tana da fadi Kuma akwai ra'ayoymabanbanta dangane da gano asalin wannan al'umma ta hausawa dalili a nan shi ne (saboda) Hausawa sun watsu a kasar Africa ta yamma a lukutta daban daban, kuma a bisa dalili daba-daban. Amma duk da haka suna tafe da wannan harshe nasu. Wato harshen Hausa shi ne sunan da suke kiran kansu da shi. Sannan da dama daga cikin wasu 'yan kabilu masu makwabtaka dasu, sun san dai akwai wasu kabilu da suke kiran su da wani suna (HABE) jukunawa na kiran su da ABAKWAI (Abakwriya) yarbawa na kiran su da GAMBARI da dai sauran su. Wato Hausawa su ne mutanen da ke zaune a kasar Hausa.

Akwai ra'ayoyi da ban-daban dangane da asalin ko gano su wanene Hausawa kamar yadda aka fada a baya. Wadannan ra'ayoyi ra'ayin  Malamm Tarihi da ra'ayin nasu nazarin harshe (harSuna) sai kuma ra'ay su kansu Hausawa dake fada a duk lokacin da aka bukaci su fadi asalinsu, wanda suke danganta shi da zuwan Bayajidda Daura.

Za mu dubi wannan ra'ayoyi na masa na tarihi dana masu nazarin harsuna kamar haka:-

2.1.1 RA'AYIN MALAM TARIHI:

Ta bangaren Malam tarihi da na masu nazarin harsuna an samu ra'ayoyi daban-daban dan gane da gano su wanene Hausawa. Wadannan malamai sun yi rubuce -rubuce da aikace-aikace masu tarin yawa dagane da gano cewa su wanene Hausawa? Saboda sun samar da ingantattun hujjoji kuma karbabbu. Dalili shi ne kuma lokacin da can, kafin karni na goma sha shidda (16 centuary) ga alama Hausawa duk da kadaitakar harshensú da al'adarsu basu hada kansu sun sami wani suna guda daya da zasu kira kansu da shi ba sai dai ya yi takama da garinsu kawai saboda tarihi ya nuna kowane gari na kasar Hausa a da can zaman kansa yake yi. Kowane sarki yana mulkin kasarsa babu wani abun da ya hada sarakuna da juna. Sai yake-yaken juna da hare-hare sai daga baya ne mamayewar mulkin baki kamar daular songhai da ta Borno da ta kwararrafa ta fara hada kawunansu. Daga nan kuma sai jihadin Shehu Usman Danfodio Ya zo ya dada hada su guri daya.

2.1.2 RA'AYIN JOHSTA

Johsta A acikin littafin sa mai suna THE FULANI EMPIRE OF SOKOTO (1969) Ya nuna cewa wani lokaci wasu mutane da ake kira Berbers sun ratso Sahara zuwa kasar bakaken fata. Suka yi auratayya da bakaken, wanda wannana shi ne ya yi sanadiyyar samuwar Hausawa.

2.1.3 RA'AYIN S.G SMITH:

A littafinsa mai suna The begining of hausa society (Asalin Al'ummar Hausawa) ya yi bayani cewa akwai kaura da ta faru daga gabas zuwa wurin da a yau ake kira kasar Hausa. Wannan kaura ta faru ne tsakanini (190-1000 AD) ya kuma nuna cewa a dalilin yin wannan kaura shi ne larabawa suka yaki mutanen Arewacin Africa. Wannan ya yi sanadin tasowar mutanen wannan wuri zuwa kudancin wurin da suke kira kasar Jukururu a nan suka yi auratayya da mutanen wurin wanda ya yi sanadiyyar sanmuwar Hausawa.

2.1.4 RA'AYIN MASANA HARSUNA

Abdullahi smith (1978) da Sultan 1979. Smith ya danganta a salin Hausawa da wani lokaci da Hausawa suke zaune a wani wuri da a yau yake a yankin kasar Nijar. Shi wannan masani ya nuna cewa kimamin shekaru masu yawa da suka shude wannan wuri ya ni' imantu da bishiyoyi da ciyayi da ruwa. Kuma bugu da kari rabin wannan wuri, yana da wata wadatacciyar korama wadda aka taba samunta a wannan wuri da ta taimaka wajen gudunmuwar da gudumuwar da kuma ci gaban al'ummar dake zaune a wannan wuri. Smith ya ci gaba da cewa daga nan kwatsan sai abubuwa suka fara zuwa. saboda sauye-sauyen yanayin na duniya wanda daga bisani shi wannan wiri ya koma sahara ita kuwa wannan kora ma sai ta kafe karkaf. kuma aka neme ta sama da kasa bata ba dalilinta a wannan yankin.

A bangaren gabashin wannan wuri bai hadu da wannan matsala ta Kafewar ruwa ba wanda a yau ake yi masa lakabi da tafkin Chad. Smith, ya nuna cewa a sanadiyyar wadannan matsaloli ne Hausawa suke zaune-a wannan wuri sannu a hankalı suka dinga kaura suna dawowa kuđancin wannan yankin saboda ganin ni'imarsa, kuma wannan Wurin Smith ya bayyana cewa wurare kamar Kano, Katsina, Daura, Zazzau, da sauransu na daga cikin wannan yanki da Hausawa suka mamaye

2.1.5 RA'AYIN MAHADI ADAMU

Ya ce idan a harshen Hausa a kace wannan bakaza ne ko waccan bakaza ce ana nufin dan kaza ko var kaza ce. Misali: idan an ce dan Badauri to ana nufin dan Daura, Bakatsine ana nufin dan Katsina, Babarbare da Babarbara ana nufin dan barbare, ba kane ana nufin dan kano, Bazazzage ana nufin dan zaria da dai sauransu. Don haka bahaushe shi ne dan kabilar Hausawa

3.0 BABI NA UKKU

3.1 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

Akwai hanyoyin da ake amfanı da su wajen gudamar da bincike, sai dai yanayin binciken da za a yi shi ke tabbatar da irin hanyar da za ayi amfani da ita wajen samun tabbataccen bayani. Akwai binciken da zai iya hada yin amfani da hanyoyi biyu koma fiye da haka Hanyoym bincike sun kunshi

I. Tattaunawa (interview)

II. Bitar ayyukan da suka gabata (literature review)

III. Lura (observation)

Iv. Tsararrun tambayoyi (questionaniars)

3.2 ΜΑΤΑKAN GUDANAR DA BINCIKE

Kowane bincike akwai irin matakı ko hanyar da ake bi ko amfani da ita domin a samu nasarar kammaluwarsa. Dangane da binciken da muka gudanar mun yi amfani da hanyoyin gudanar da bincike kamar haka:-

a) Bitar ayyukan da suka gabata (literature review)

b) Tattaunawa (interview)

c) Lura (observation)

3.3 TSARIN GUDANAR DA BINCIKE

Domin samun nasarar kamala kowane irin bincike, ya za ma wajibi a tsara shi, yadda za ya bada damar bin diddikin ko gano matsalar binciken ko gudanar da hakan mun tsara bincıkenmu ko gudanar da shi ta hanyar-

a) Ganawa ko tattaunawa da jama'a, mutanen da suke dattawa da kuma dalībai masu nazarin Harshen da dai sauransu.

b) Tsaran tambayoyi da ake tsarawa a tukarda don a samu kammalallen sakamakon Wato (questionnaires)

4.0 BABI NA HUDU

Tasirin Zamananci akan canfe-canfen Hausawa

4.1 TASIRIN ZAMANANCI GA AL'AUMMAR HAUSAWA. Bahaushe shi ne dan kabilar Hausawa, kuma cikar kamalarsa ta Hausawa mai Magana da Harshen Hausa. Yana kuma gudanar da al'adun Hausawa a duk in da yake ko ya tsıncı kansa da kúma dukkan wani matsayın da ya samu a rayuwarsa ta yau da kullum, haka kuma, ba ya kyamar al'adun 'yan uwansa na kauye da kuma dukkanin mu'amulolin Hausawa mai wannan shi ne ake kira Bahaushe wannan zamani ya yi tasiri matuka ga al'umar Hausawa.

Dangane da Hausawa za a iya ganin ga tasirin zamani ta fuskar fiddo da wadansu muhimman abubuwa wadanda suka hada ko suka shafi al'ada da tarbiyya da addini da wayar da kai da kasuwanci da kiwon lafiya, da zamantakewa da iliimin boko da sauransu, zamu kallesu daya-bayan daya

4.1.1 TA FUSKAR AL'ADA

Dangane da tasirın, da zamanı ya yı a kan al'ummar Hausawa, ya yi tasiri kwarai ta fuskar canza masu al'ada daga tsuhuwa zuwa sabuwa, Idan aka yi la'akari da yadda al'adu suke a da sun sha banban da na yanzu. Misali

Wankan jego; a da idan mace ta haihu sai ta yi wankan jego amma yanzu zamani ya canza shi zuwa shan magani bature.

Karatun allo A da muna kai ya'yanmu makarantar allo, amma zuwan zamani ya canza shi zuwa makarantun islamiya.

4.1.2 TA FUSKAR TARBIYA

Tafuskar tarbiya zamani ya taka rawa kwarai, saboda ıdan aka duba a nan tarbiyar da take da ta sha banban da ta yanzu, akwai wayewa da kuma addini a tare da ita.

Misali:

- Idan Uba ya mikawa dansa Hannu ba zai amsa ba saboda yana ganin ya yi rashin kunya. Amma yanzu sakamakon Ilimin Addini idan uban ne da kansa ya mikawa yaron yana iya amma babu laifi.

4.1.3 TA FUSKAR WAYAR DA KAI

Zamani ya yi tasiri ta fuskar wayar da Kan jama'a ta hanyar kawo sabbin abubuwa wadanda suka hada da aika sakonni da tafiye-tafiye da abubuwan mare rayuwa.

Misali:

- Sakonni a da cen ana tura mutum saman doki ko jaki ko rakumi ko a kasa wanda yanzu da mota ko jirgin sama ko na kasa ake yi ko a aika ta kafar sadarwa irinsu radio da talabijin da makamantansu.

4.1.4 TA FUSKAR KIWON LAFIYA

Zuwan zamani yasa an samu hanyoyi da dama ta yadda mutane za su rika kula da lafiyar su amma a da cen kiwon lafiya yana da matukar wahala ga al'ummar Hausawa musamman ta fuskar ruwan sha da abinci. Amma bayyanar zamani ya kawo chanjin ruwa zuwa na fanfo da asibiti da gine-ginen zamani ba irin da wancen lokacin ba.

4.1.5 TA FUSKAR KASUWANCI

Idan aka yi duba da yadda ake aiwatar da kasuwanci a wancen zamanin za aga an samu babban cigaba da bunkasa da yawa sana'oim Hausawa zamani ya yi tasiri a cikinsu. Misali kamar sana'ar Kira yanzu ta koma Walda da sana'ar Saka ita ma yanzu an samu mashina na zamani masu amfani da wutar lantarki cikin sauki da sauri.

MATSAYIN CANFE-CANFE A AL'UMMAR HAUSAWA JIYA DA YAU

A cikin wani bayani da aka gabatar a wata mukala an bayyana cewa canfi yana da matsayi a al'ummar Hausawa yana da muhimmanci musamman idan aka yi duba da matsayin da su Hausawa suka bashi a rayuwarsu ta yau da kullum. Kafin zuwan addinin musulunci wato lokacin Al'ummar Hausawa basu da wani tafarki na rayuwa mai dokoki zayyanannu irin na addinin musulunci. Sai dai kawai tafarkin rayuwa irin na gargajiya Wanda tushensa ya samo asali daga al'adar canfi.

Al'adar canfi a da kafin zuwan musulunci tare da shigar Hausawa cikinsa sun dogara ne da canfi wajen samar da dokoki da ka'idojin rayiwarsu. Don haka canfi shi ne a matsayin addininsu da shi su aiki wurin yin umarni da kuma yin hani a tsakanin su.

4.2. CAMFI KAFIN ZUWAN MUSULUNCI (JIYA)

Kamar yadda aka ambata ne tun farko cewa Canfe-Canfen Hausawa sun kirkire su ne kafin shigar su cikin addınin musuluncı. Don haka Canfi a wancan lokaci yana da babban matsayi a rayuwar Hausawa, musamman idan muka yi la'akari da cewa wancan lokacı Canfe-Canfe suna a matsayin dokoki ne da ka'idoji a tafiyar da rayuwar al'umnar Hausawa. Haka kuma, canfi ya yi tasiri a kan Hausawan, domin kuwa duk wani abunda Canfi ya shinfida a cewa ayi ko labari. Bahaushe mutun a wannan lokacı ya na kokarin ganın ya gujema wanan abun ba don komai ba sai dan gudun abinda Canfi ya fada ga wanda ya karya dokar ko ka'idar da canfin ya shinfida. Wannan kuwa ya biyo bayan yadda da canfi da kuma tsananin tsoron sakamakon yadda canfin musamman idan muka dubi sigar canfi tafuskar tsanani wajen yanke hukunci.

Alal misali, kusan duk wani canfi da muka duba za mu ga cewa, idan sakamakon sa wadanda ake so ne ana tsananta kyautata sakamakon fiye da kima. Ana iya samun haka a canfin mai cewa duk wanda ya ci goro har ya yi masa kitse to zai shiga aljanna kai tsaye. Don haka irin wannan sakamakon, shi ya kwadaitar da Hausawa yadda da canfi Haka kuma, idan sakamakon ba wanda ake so ba ne, ana nuna munin sakamakon fiye da kima. Alal misali, canfin nan mai cewa "duk wanda ya kife iskar guguwa da kwarya, idan ya bude bayan ta wuce zai ga jariri, to amma ba zai kai labari ba, zai mutu da kuma tasirin yarda da mutanen boye (iskoki) a zukatan al'ummar Hausawa shi ya sa Hausawa suka yı imani da irin wannan canfi. Don haka ta hanyar amfanı da irin wannan hikimomi na danganta sakamakon canfi da abubuwa na al'ada masu tsiri a kan Hausawa ya sa canfin kansa ya yi tasiri a kan Hausawa. Alal misali Asali da tasirin canfe-canfe ne a kasar Hausa aka ki jinin mahauta ba don komai ba sai don canfa su da cewa su ba matane ne ba, don kuwa wai ranar tashin kiyama za a tashe su karnuka ba mutane ba. Haka an ce wai idan aka rarike kara ka leki mahauci ta cikin kofar karan za ka ganshi da wutsiya da kai irin na kare. Amma fa wai idan ka gani za ka mutu:

4.2.3 CANFE-CANFE BAYAN ZUWAN ADDININ MUSULUNCI ( YAU).

Addinin musulunci addini ne Wanda Allah ya aiko Manzonsa Annabi Muhammadu tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi, zuwa ga 'yan Adam baki daya. Haka kuma addninin musulunci yana koyi da bauta wa Allah shi kadai. Tare da yin imanin cewa shi kadai yake bashi da abokin tarayya kuma shi kadai yake da ikon rayawa da kashewa da azirtawa da talautarwa da dukkan abubuwa na kaddara. An samu cewa addinin musulunci ya zo kasar Hausa a viking karni na Goma sha biyar.

A sakamakon shigar Hausawa cikin Addinin musulunci tare da samun ilimin addinin ya haifar da samun Karin wasu canfe-canfe da suka zo da kalamai na addini wadanda suke da tasiri Sosai a rayuwarsu ta yau da kullum. Don kuwa addinin musulunci bayyanannen al'amari a cikin littafin Allah mai tsarki. Don haka a matsayin canfi na kagaggen bayani akan wani abunda za a yi ko kuma zai faru da ya kunshi sakamakon wani abu in ya faru. Wannan ya raunana Sosai a cikin zukatan Hausawa Musamman bayan da addini ya yi bazu ko'ina a cikin Hausawa da samun ilim tauhidi Wato kadaita Allah daya ne, kuma kowa da komi nasa ne shi ne mai rayawa kuma mai kashewa. Ba ta hanyar tsafi ko canfi ko bori ba kamar yadda sukai amanna Kafin zuwan addinin musulunci a cikinsu. Anan an samu wasu canfe-canfe da suka tabbatar da wannan.

Misali

- Canfin nan da ke cewa idan aka haifi yaro ranar Asabar zai rika samun hadari akai-akai a rayuwarsa.

- idan hannun mutum yana kai-kai zai samu kudi.

- Idan mutum ya fito daga gida zai yi tafiya ya fara haduwa da kuturu to wannan tafiyar babu sa'a a cikinta.

Idan aka dubawa wadannan canfe-canfe sun kaucewa ka'ida musulunci da kuma imani da kaddara domin duk abunda ya samu mutum daga Allah ne babu Wanda zai iya dorawa mutum wani abu mai kyau ko mara kyau sai Allah shi kadai.

Amma duk da shigar Hausawa cikin addinin musulunci bai sa sun yi watsi da al'amarin canfi ba gaba daya ba dole sai anga tasirinsa a wurinsu. Kamar yadda Malam Muhammad Balarabe Umar ya fada

'' wani abu mai ban mamaki dangane da canfi shi ne yana da wuya a samu wata al'umma da zata ce tabar canfi komi zurfin da ta yi wajen karbar wani addini ''.

4.4 TASIRIN ZAMANANCI A KAN CANFE-CANFEN HAUSAWA.

Al'adar canfi a rayuwar Hausawa tana da muhimmancin gaske musamman idan muka yi La'akari da matsayin canfi a rayuwar su ta yau da kullum kafin addini Hausawa basu da wani tafarkin rayuwa mai Dokoki zayyanannu irin na zamani sai dai kawai tafarkin rayuwa irin na gargajiya wadda tushenta ya samo asali daga al'adar canfi. Kafin zuwan Zamani tare da shigar Hausawa cikin Zamani tana da muhimmanci don kuwa a kanta ne al'ummar ta dogara wajen samar da dokoki da ka'idojin rayuwa. Don haka akwai tasirin yarda a cikin lamarin canfi. Wannan imani na yarda da canfi ta hanyar yin amfani da wasu abubuwa masu tasiri a rayuwar al'umma da abin ya fuskanci munana wani abu dake tsakanin su, idan mutum ya aikata wani abu da al'ummar bata so ko kuma ta hanyar kyautata sakamakon wani abu da al'ummar ta ce tsakanin su ayi. Musamman sun yi kokarin danganta canfi da irin sigar da muka rigaya muka san can fi da shi. Wato na kokarin hani ga al'ummar daga wata xabi'a da al'umma bata so ta hanyar tsoratarwa.

Bunza (2006) ya bayyana irin tasirin da zamani ya yi akan Hausawa inda yake cewa al'ummar Hausawa tafiya take yi tana yalwa da bazuwa a uwa duniya. Ganin haka ya sa na ware wannan fasali da yi masa suna da cewa canfin zamani, ko canfe-canfen zamani. A nan ina nufin duk wani canfi da Bahaushe ya kago ko ya samu a cikin zamani ko bayan bayyanar Turawa har zuwa wannan lokaci. A takaice wannan rukunin canfe-canfe na Hausawa ya bayar da gudummuwa wajen canza ko sauya tare da bijiro da sabbin canfe-canfe a rayuwar Hausawa.

Misali:

- Idan Direba ya kabe Agwagwa da mota zai samu mummunan Hadari.

- Kallon majigi ga mace mai ciki yana sa a haifi yaro mahaukaci.

- Magana da amsa kuwa na samar da cutar kuturta.

- Duk Wanda ya tsufa cikin siyasa cikin talauci yake mutuwa.

- Wanda duk aka yi wa aikin asibiti baya kara lafiya.

Idan aka yi La'akari da wadannan misalai za a ga cewa bunkasar Zamani ne yasa aka samu irinsu sakamakon haka zamu iya cewa Zamananci ya taka muhimmiyar rawa a kan al'ummar Hausawa a cikin al'adunsu na canfe-canfe.

4.5 MUHIMMANCIN CANFE-CANFE

Ko wace irin al'adar da mutane suke aiwatar wa ba a rasa wasu alfanoni da ake samu a cikinta. Amfanin ya dogara da abin da masu al'adar ke cewa. Amfani ko muhimmanci a fahimtar al'adarsu Daga cikin Muhimmancin canfe-canfe a rayuwar Hausawa akwai:

1. Koyar da Tarbiyya

2. Inganta kiwon lafiya

3. Kaifafa tunani

4. Kyautata Tarihi

5. Adana Al'ada da raya ta

6. Gyara zamantakewa

7. Inganta Imanin Bahaushe

4.5.1 KOYAR DA TARBIYYA

A cikin canfe-canfen a kan tsinci wasu dake koyar da yara biyayya ga magabata da mabiyansu. Musamman idan muka yi Nazarin wadannan canfe-canfe masu zuwa:

1. Idan yaro yana duban al'aurar manya zai yi bununuwa.

2. Idan yaro na taba hular manya rangwangwan zai kashe shi.

3. Idan namiji na cin abinci da mace za ta kwace masa karfi.

4. Idan mutum yana rantsuwa da damina kwarankwatsa za ta fado masa.

5. Macen da ta ki yi wa mijinta durkuso kafafu tsaitsaye take mutuwa.

4.5.2 INGANTA KIWON LAFIYA

Tattalin kiwon lafiya na daya daga cikin abubuwan da Bahaushe ke ba muhimmanci a rayuwarsa. Akwai tarin canfe-canfe da suka tabbatar da haka daga ciki akwai irinsu:

1. Shara da daddare tana kawo tsiya.

2. Barin kwarkwata a ka na kawo girgizar kasa

3. Idan mace mai ciki ta je rafi dibar ruwa da dare to aljanu za su canza mata yaro ta haifi Dan ruwa.

4. Idan mutum na iza wuta da kafa maye zai kama shi

5. Idan mutum yana tafiya da takalmi kafa daya to wai yana kirga kwanakin mutuwarsa.

4.5.3 KAIFAFA TUNANI

Daga cikin canfe-canfen Hausawa akwai masu sa shi ya yi zurfin tunani irin na kakalo wasu abubuwa da zasu amfane shi ko su amfani al'umma. Misali

1. Shan miyar kuka na sa basira

2. Zama da janaba a jiki na kawo farfadiya

3. Yawan bacci da Rana ya kawo lafiya

4. Cin abinci ba a sha ruwa ba na kawo jin yunwa da wuri

5. Yin fitsari a tsaye na kawo tsiya.

4.6 ILLOLIN CANFE-CANFE

1. Haddasa gaba a tsakanin al'umma. Misali a dalilin canfi ne a kasar Hausa aka ki jinin Mahauta ba don komi ba sai don an canfe su da cewa su ba mutane bane don kuwa wai ranar tashin kiyama za a tashe su da siffar karnuka ne ba ta mutane ba.

2. Karya. Yana da yin karya da fadar abunda ba gaskiya ne ba. Misali zaka ga Abu ba haka yake amma ace in ka yi shi lallai abu zai same ka Bahaushen mutum a da bai yarda ya zauna maka akan murhu ba saboda ya yarda cewa idan ya aiwatar da hakan asirinsa zai kare.

3. Yana haddasa taurin kai: Canfi ya Dade a cikin zukatan Hausawa Wanda yayi tasirin da masu jahadi suka sha wahala sosai wurin kiransu zuwa ga addinin Allah.

4. Yana kawo shirka: haka kuma canfi yana sa al'ummar Hausawa su yi shirka. Ma'ana su danganta wani abu da Allah, Misali Bokaye idan suna neman wani abu sukan roki aljanu ne maimakon Allah Allah domin biyan bukatarsu.

5. Yana gurbata lafiya: haka kuma al'ummar Hausawa sun yi imani da cewa duk Wanda ya yawaita cin goro har ya yi masa kitse sai shiga Aljanna kai tsaye bayan kuma duk Wanda ya cika cin goro zai zamar masa illa.

BABI NA BIYAR

Kammalawa

5.1 TAKAIRAWA

Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da Amincin sa su tabbata ga Annabi Muhammadu (SAW) Wanda cikin taimakon sa ne ya bamu damar fara wannan aiki da kuma kammala shi. Kamar yadda ya gabata a babi na daya mun gabatar da dalilai da manufofin bincike.

A babi na biyu kuwa an gabatar da bitar Ayyukan da suka gabata dangane da canfe-canfe tare da Ma'anar tasiri da Ma'anar Zamananci da kuma bayyana su wanene Hausawa, binciken ya ci gaba da bayyana ma'anar canfe-canfen da kuma kawo ire-iren canfe-canfe. Sannan a cikin babi na ukku an gabatar da irin hanyoyin da aka bi wurin tattara bayanai da matakan da aka bi domin gudanar da bincike. A kuma cikin babi na hudu mun gabatar da irin tasirin Zamananci a kan canfe-canfen Hausawa da matsayin canfe-canfe a wurin al'ummar Hausawa da bayyana tasirin Zamananci akan canfe-canfen Hausawa tare da kawo Muhimmancin sa da kuma illolinsa. A cikin babi na karshe na wannan aiki an yi bayanin shawarwari da takaitawa da kammalawa da kuma manazarta.

5.2 KAMMALAWA

Wannan bincike za a iya kammala shi ta bayyana tasirin Zamananci a kan canfe-canfen Hausawa kamar haka:

Binciken ya gano irin matsayin da canfi yake da shi a cikin al'ummar Hausawa da kuma irin yadda Hausawa suka dauki canfi a cikin rayuwarsu.

Binciken ya gano ire-iren canfe-canfe da ake da su a cikin al'ummar Hausawa da kuma fito da illolinsa da muhimmancin sa a wurin Hausawa.

5.3 SHAWARWARI

Dangane da wannan bincike zamu iya bada shawarwari ga duk Wanda ke San yin bincike a wannan fili kamar haka:

A na iya yin bincike akan illolin canfe-canfe a rayuwar Hausawa

Yana da kyau a rika koyar da darasi akan canfe-canfen Hausawa domin warware wa mutane abin da ya shafi canfi da Wanda ba canfi ba.

Ana iya yin bincike domin gano muhimmancin canfe-canfe ga al'ummar Hausawa

Yana da kyau ayi bincike domin gano irin rawar da canfi yake rakawa a rayuwar al'ummar Hausawa

Yana da kyau a rika samun mawallafa su rika wallafa Littattafai a kan canfi domin wadatar da masu nazari ko bincike da kuma inganta al'adar Hausawa gaba daya.

 MANAZARTA

Adamu M (1991). The Hausa factor in West African History. Ibadan: Printed in Nigeria by the Caxton press (West Africa) Limited Ibadan

Bunza AM (2006) Gadon fede Al'ada Lagos: Tiwal Nig Limited

Dangambo A (1998) Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmancin sa ga Rayuwar Al'ummar Hausawa. Kano Nigeria sashen koyar da Harsunan Nijeriya Jami'ar Bayero kano

Fagge UU (1982) Ire- Iren Karin Harshen Hausa na Rukuni Kano Published by Benchmark publishers Limited.

Jingir SA (1982) Zaman Hausawa da Al'adunsu Zaria Gaskiya Publishers priority press Zaria Post a Comment

0 Comments