TAMBAYA (122)❓
Mene ne gaskiyar binciken da
masana sukai akan cewar an gano wata Rana mai haske ta daban a sararin
samaniya. Hakan na nufin ba iya wannan ranar bace a saman duniya ba kenan?
✍️AMSA A TAQAICE:
(Akwai ayoyin Allah a sammai da kassai wadanda Shi kadai ya barwa kanSa sanin adadinsu. Rana daya daga cikin taurari ce dake sararin sama'ud dunya, nisan nisan dake tsakaninmu da sama ne ya sa ba ma iya ganin sauran ranakun. Imani da Allah shi ne yafi muhimmanci fiye da yawan tambaya akan ayoyinSa)
Bismillahir Rahmaanir Raheem
Tabbas, Rana (Ash-shams) ba guda
1 ba ce a sararin samaniya kamar yanda wasu mutanen suke tunani. A binciken da
Astronomers (masana kimiyyar sararin samaniya) suka gano ta hanyar amfanida
na'urar Hubble Telescope, akwai Miliyoyin ranaku a iya birnin taurarinmu wato
Galaxy dinmu (da ake kira da Milky Way Galaxy) kuma an gano cewar da akwai
Galaxy sama da miliyan dari a sararin sama. Ranarmu da muke iya gani a sararin
samaniya tanada nisan shekarun haske (light years) na kusan shekaru 27,000
(Dubu ashirin da bakwai) daga tsakiyar Galaxy dinmu. Amman wani ikon Allah
hasken nata yana karasowa duniyarmu ne a cikin mintuna 8 kacal
Kafin na gindayar da mai tambaya
yakamata nayi bayani dalla dalla akan batun mene ne shekarun gudun haske (light
years). A cikin 1 second (sekon 1) na agogo, haske yana gudun 300,000km
(kilometer dubu dari 300). Misali: ka qaddara kana aiki a company NEPA, wutar
lantarkin da ka kunna daga Nigeria zata isa kasar Niger a kasada 1 second (ma'ana
kafin ka qifta ido har yan Niger sunga ankawo wutar)
Kenan a cikin second 1 kacal
haske zai iya zagaye duniya sau 7 (300,000km arabata gida 22 zai zamo 13,636km,
wanda fadin duniyarmu a diameter shine 13,500km). A lissafin circumference
kuma, duniyarmu takai 40,075km, wanda ahakan kana kunno haske zai zagayata sau
7 a cikin second 1 kacal. A taqaicedai gudun haske ya zarce na bindiga, jirgin
sama, da kuma rocket. Wannan lissafin second 1 muke, ita kuma rana tanada
tazarar shekaru 27,000 na gudun wancan hasken, bawai seconds, mintuna, kwanaki
ko watanni ake magana ba, shekaru 27,000 ake magana anan. Allahu Akbar!
A wannan matsanancin gudun da
takeyi kuma bata cin karo da wata tauraruwar a sararin samaniya
(Alhamdulillah), kuma a hakan wasu taurarin suna daukeda cincirindon duniyoyi
wadanda suke daukeda watanni a tattaredasu. Kuma ko wannensu dawafi (bautar
Allah) suke a kewayen duniyarsu. Solar system dinmu tana jujjuyawane a salon
juyawar helix/spiral (helix motion) ma'ana katantanwa take tana juyawa a duk
awanni 24 (24 hours da muke kira da kwana daya). Misali: ka samu ranwa, ka
garata a kas, zakaga tana juyawa, kamar hakane duniyarmu take juyawa
Wani zaice "Yanaji bana
juyawa kuma alhalin ance duniyar tana katantanwa?" Amsar shine
"Gravity kokuma kace maganadisu ne yasa baka jin juyawar" Astronomers
sungano cewar Rana (Ash-shams) tana ninqaya a sararin samaniya kamar yanda mai
iyo yake ninqaya a cikin ruwa. Samada shekaru 2,000 da suka gabata lokacinda
mutane irinsu Aristotle suke tunanin Duniya ba ta da farko kuma ba ta da
karshe, Rana kuma a tsaye take qiqam, Allah SWT ya fada a cikin Qur'ani mai
girma, cewar Rana tana ninqayane a sararin samaniya. Allahu Akbar!
Hujjar hakan tana a cikin Suratu
Yasin ayata 38:
( وَالشَّمْسُ
تَجْرِي لِمُسْتَقَرٍّ لَّهَا ۚ ذَٰلِكَ تَقْدِيرُ الْعَزِيزِ الْعَلِيمِ
)
يس
(38) Yaseen
"Kuma rãnã tanã gudãna zuwa
ga wani matabbaci nãta. Wannan ƙaddarãwar Mabuwãyi
ne, Masani"
Ayata 39 kuma yace:
( وَالْقَمَرَ
قَدَّرْنَاهُ مَنَازِلَ حَتَّىٰ عَادَ كَالْعُرْجُونِ الْقَدِيمِ
)
يس
(39) Yaseen
"Kuma da watã Mun ƙaddara
masa manzilõli, har ya
kõma kamar tsumagiyar
murlin dabĩno wadda ta
tsũfa"
( لَا الشَّمْسُ
يَنبَغِي لَهَا أَن تُدْرِكَ الْقَمَرَ وَلَا اللَّيْلُ سَابِقُ النَّهَارِ ۚ وَكُلٌّ
فِي فَلَكٍ يَسْبَحُونَ )
يس
(40) Yaseen
"Rãnã bã ya kamãta a gare
ta, ta riski watã. Kuma dare bã ya kamãta a gare shi ya zama mai tsẽre wa
yini, kuma dukansua cikin sarari guda suke yin iyo"
Allah SWT wanda shine ya halicci
sammai 7 da kassai 7 da abunda ke cikinsu da tsakaninsu, ShiNe ya fada a cikin
Littafin (Qur'anin) da aka saukar dashi qarni 14 (shekaru 1,400) da suka
gabata. Gashi kuma Astronomers sun gano hakan kwanannan ta hanyar amfanida
Hubble Telescope. Wannan ayar ta 40 da tayi magana akan iyo (swimming) kadai ta
isa ta tabbatar maka da mu'ujizar Al-Qur'ani mai girma
Ba ma gano wata rana ne abin
mamaki ba. Kwanannan Professor Michau Kaku (malami a wata jami'a dake kasar
Amurka) ya ce sun yi amfani da na'urar JWST (James Webb Space Telescope) sun
gano wata Rana a sararin sama, duniyoyi guda 5,000 (dubu biyar) suna zagayeta
kamar dai yanda duniyarmu take zagaye ranarmu (ash-Shams). Wannan duk ikon
Allah ne jibge a sararin saman duniyarmu. Duk don su zame mana ayoyi akan
samuwarSa (Subhanahu wata'ala) kuma don su tuna mana dalilin da yasa ya halicce
mu wato mu bauta masa Shi kadai ba tare da yin shirka ba
A kowanne hali muka tsinci kanmu
kada mu sake mu manta aya ta 2 dake cikin Suratu Mulk:
( الَّذِي
خَلَقَ الْمَوْتَ وَالْحَيَاةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا ۚ وَهُوَ
الْعَزِيزُ الْغَفُورُ )
الملك
(2) Al-Mulk
"Shi ne Wanda Ya halitta
mutuwa da rãyuwa domin Ya jarraba ku, Ya nũna wãye daga cikinku ya fi kyãwon
aiki, Shi ne Mabuwãyi, Mai gafara"
Ya Allah ka bamu ikon bauta maka
ka rabamu da shirka da bidi'a ka tabbatar damu akan musulunci kan tafarkin
Sunnah bisa fahimtar Salaf
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa:
Usman Danliti Mato
(Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.