Ticker

6/recent/ticker-posts

Suna Watanni Shida (6) Kafin Su Ga Faduwar Rana. Ya Za Su Yi Azuminsu

TAMBAYA (86)

Aslm. Iftar mubaraq. Inada tambaya su wadanda suke kamar a norway ya zasuyi azumi, tunda kafin suga faduwar rana sai sunyi wata shida

AMSA

Alhamdulillah

Allah Subhanahu wata'ala yace

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ )

البقرة (183) Al-Baqara

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa,

Don haka su ma Norwegians hukuncin ya hau kansu duk da cewar zasu share darare 180 (rabin shekara) a cikin dare ba tare da sunga ko da kyallin hasken rana ba

"Allah daya gari ban-ban" karin maganar bahaushe

Nasha cin karo da tambayoyi daga dalibaina na secondary school kamar: "To yan kasar Norway din zasu share wata 6 suna bacci ne, su farka idan safiya tayi ?", yan anguwarmu sukan tambayeni "To a cikin dare kenan suke gudanarda bukukuwan karamar sallarsu idan watan 1 ga Shawwal ya kama ko kuma hakuri suke da bikin sallah tunda yazo musu a cikin dare ?"

Bari na amsa tambayar "Musulman da suke a kasar Norway ta yaya zasuyi azumi tunda kafin suga faduwar rana sai sunyi wata 6 ?"

A shekarar 1980 babu musulmai sosai a yankin Arctic Circle (doron duniya daga saman kudanci, domin gane bayanin: ka kaddara a hannunka akwai kwai dafaffe to can saman tudunsa shine kamar yankin kasashen Arctic kasar Norway tana cikinsu yayinda kasansa kuma shine arewacin Antarctic), musulmai sun fara hijira ne daga kasashen Somalia, Iraq, Pakistan zuwa kasashen Sweden, Norway dakuma Finland, wannan shine silar yawaitar al'ummar musulmai a kasashen da ake share watanni a kalla 6 ba'aga hasken rana ba, haka watanni a kalla 6 a cikin dare

Wani musulmi mai suna Hassan Ahmed, wanda aka yiwa irin wannan tambayar a garin Tromsø, wanda gari ne a tsakiyar kasar Norway 350 kilometers daga Arctic Circle, mutanen garin yawancinsu yan gudun hijirane daga kasar Somalia, da yawan musulmai bai wuce 1,000  ba, wanda Hassan yayi bayanin cewar rana bata faduwa har watan Ramadan ya wuce

Ya ci gaba da cewa "Munada fatawowi guda 2 da malamai suka bamu kodai mu dinga azuminmu da kasar musulmai dake makotaka damu ko kuma mu dinga amfani da lokacin Makka"

An tambayi Sandra Maryam Moe, wadda ta bata dade da amsar musulunci ba (revert) wadda ta kasance manager ce a Tromsø community center tace "Tunda a cikin dare zamu dinga rayuwa har watan Ramadan dinnan ya kare, sai muka zabi amfani da lokacin Makka"

Hakan yana nufin idan rana ta fito karfe 5:00 am (na asuba) a Makka to mutanen Tromsø sai su fara azuminsu daga karfe 5:00 am irin na kasar Norway (Norwegian time)

"Dadin dadawa hakan yafi kwanciyar hankali da nutsuwa garemu saboda Makka suna da kayyadadden lokacin (timetable) na fitowar rana da kuma faduwarta hakan yasa da sallar da azumi suka daidaitu" inji Sandra Maryam Moe

A daren karfe 7:07 pm na Tromsø musulmai sukan tarune a masallachin Alnor suyi iftar dinsu alhalin suna shan ruwa amman suna ci gabada ganin hasken rana ta cikin windunan masallachin

Moe ta ci gaba da cewa "Kullum da daddare mukan cika anan musha ruwa tare muyi sallah tare, lokaci ne na annashuwa a garemu a gaba daya watan Ramadan din"

Wani zaice to meyasa su wadannan kasashen suke samun irin wadannan lokatai, sai muce ai saboda karkacewar da duniya tayi na 23.5° shine yasa ake samun yanayi guda 4: Summer: zafi, sai Winter: sanyi, da kuma Autumn: rani, sai kuma Spring: damina. A shekara kusan gaba daya sassan duniya guda 4 (banda Arctic da Antarctic) suna karban hasken rana kai tsaye ta yanda idan hasken rana ya hasko yankin arewa, su kuma kudancin duniya zasu ji sanyi haka kuma idan ta haske kudu, su kuma yankin arewa zasu ji zafi, wannan shine dalilin da yasa kasar Norway take share watanni 6 kafin rana ta haskota hakama watanni 6 kafin dare ya gushe. Allahu Akbar ! Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin mafadan rana 2 da mahudanta 2

To a takaice dai wannan shine amsar lokacin da yan kasar Norway suke shan ruwa bayan sun kammala azumi alhalin basa ganin fitowar rana sai an share watanni 6 haka kuma idan rana tayi basa kara ganin faduwarta sai wasu watanni 6 din sunyi

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments