TAMBAYA (85)❓
Wanne aiki ya kamata mu dinga yi don samun falalar goman
karshe ?
AMSA❗
Alhamdulillah
Uwar Muminai, Nana Aisha (Radiyallahu anha) ta tambayi
Annabi Sallallahu alaihi wasallam: "Ya Ma'aikin Allah, shin me zan fada
idan naga daren Lailatul Qadri ?" Sai yace: "Kice
اللّٰهُمَّ
إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّيْ
Ma'ana: "Ya Allah kai Mai Afuwa ne, kuma kana son yin
afuwa. To kayi afuwa gareni"
Imam Abu Dawud ne ya rawaito shi, da Tirmidhi da Ibn Majah
Dangane da aiki kuma. Ga bonanza kamar haka;
A shawarce anso mutum ya dinga ciyarwa idan kana da iko. Ko
kuma ka dinga siyan dabino ko da na Naira 100 ne a kowacce rana a cikin goman
karshennan. Domin kuwa indai har aka dace a ranar Daren Lailatul Qadri ka bayar
to wannan ladan dabinon zai zamo kamar kayi kyauta ne ta tsawon shekaru 84 da
watanni 6
Babbar garabasa kuma itace ka gina gidaje a cikin Aljannah
Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace: "Duk mutumin da
ya karanta Suratul ikhlas (Qulhuwallahu ahad) sau 10 a jere, Allah Azzawajallah
zai gina masa katafaren gidan bene a cikin gidan Aljannah" Sai Sayyadina
Umar yace: Ya Rasulullah gidan bene, aikam zamu yawaita karantawa. Sai Annabi
Sallallahu alaihi wasallam yace: "Fallahu aksar" Ma'ana: Allah shine
mai yawaitawa
Duba hadisin a cikin Sahih al-Jami' as-Saghir lamba ta 6,472
na Shaikh Muhammad Nasiriddin al-Albany (Rahimahullah)
Kenan indai muka dage da karanta Qulhuwallahu ahad sau 10 a
jere, kuma muka dace da wannan daren to Allah (Subhanahu wata'ala) zai gina
mana gidaje dayawa sau adadin kwanakin dake cikin shekaru 84 da watanni 6
dinnan. Ba fa a kasar Dubai ba, a'a gidajen bene na alfarma a Aljannah ake
magana. Allahu Akbar ! Me yafi wannan ?
Muna roqon Allah ya bamu ikon aiwatarwa. Sannan kuma kada mu
manta mu dinga saka yan uwanmu musulman Gaza dake kasar Palestine da ma sauran
musulmai a cikin addu'o'inmu akan Allah ya kawo musu daukin kashe-kashen da
Banu Isra'ela suke musu. Sama da mutane 20,000, musulmai musamman yara, wadanda
aka kashe, tsawon watanni 6 kenan, muna roqon Allah ya karbi shahadarsu. Mu
kuma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani
Muma kuma a ci gaba da sakamu a addu'a musamman ma Malam
Khamis da yake aiki tuquru ba dare ba rana, Allah ya biyashi da Aljannatil
Firdous, Allah ya tabbatar damu akan wannan da'awa da mukeyi yasa mu dinga yi
da ikhlasi ya rabamu da riya
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.