Ticker

6/recent/ticker-posts

Ma'anar Wasu Kalmomi A Harshen Hausa

1. Ƙahon Dandi; Jin ɗumi kusa da wuta, musamman lokacin sanyi, ko ma duk lokacin da ake jin sanyin.

 2. Zunguru; Wani abu ne, dangin ƙwarya, mai ɗan tsayi da ake yi masa ƙofa daga sama a rarake cikinsa, mata kan cusa hannunsu a ciki zuwa guiwar hannu, bayan an zuba kwaɓaɓɓen lalle domin yin ƙunshi.

 3. Azargagi; Dogon zare ko tsumman da aka kekketa aka kuma ƙulla suka yi tsawo. Mata na amfani da shi wajen tufke ledar da suka naɗe ƙafafu da ita yayin ƙunsa lalle (kamar yadda yake a wannan labari, amma ya na da wata ma'anar ta daban).

4. Mazari; Ɗan tsinke ne na Itace kamar tsintsiya, amma ya fi tsintsiya ƙwari, an haɗa shi da dunƙulen laka, ya na da tsini daga ƙasa. Ana amfani da shi wajen kaɗi ko murza auduga ta koma zare.

 5. Taskira; Ɗan kwando ne ƙarami mai ɗan faɗi da ake saƙawa da Kaba, sa'annan sai a shimfiɗa masa ƴan jemammun fatu a cikinsa. A saman fatar da aka shimfiɗa ake murza mazari wajen kaɗi. Mata kuma kan yi amfani da shi wajen ajiya, sai a ɗaga fatun a ɓoye abin da ake son ɓoyewa tsakanin fatun nan, wasu na kiransa "Tayani." Akwai kuma wani ɗan kwando na Kaba mai marfi da ake sargafewa a jikin bango ana ajiya a ciki, wasu na kiransa "Taskira."

 6. Abawa; Zaren da aka samar daga taffa (audugar da aka cire wa ƴaƴa) ta hanyar kaɗi da mazari.

 7. Akwasa; Wani Ice ne da aka sassaƙa, ya na da tsayi da ɗan faɗi kamar dai Takobi. Mata na amfani da shi wajen saƙa.

 8. Gafaka; Jakar da aka yi daga fata domin adana littattafai.

 9. Agalemi; Fatar Akuya ko rago da ba a jeme ba har suka bushe (buzu).

10. Akushi; Mazubin abinci da aka sassaƙa da Itace (kwanon cin abinci na Itace).

11. Ƙoshiya; Cokali na Itace.

12. Gidauniya; Ƙwaryar da ake zuba wa maigida fura a rufe da faifai.

13. Tarde; Wani ɗan abu ne da ake saƙawa da kaba a zagaye kamar gammo. Ana ajiye Gidauniya a sama don kada ta ɓingire. Matan Fulani ma na amfani da shi wajen tallar nono, idan za su ajiye ƙwaryar nono sai su ajiye shi ƙasa, su girke ƙwaryar kansa.

14. Jemo; Shi ne matsayin kofin shan ruwa a yanzu. Da ƴar ƙaramar ƙwarya ake yinsa, girmansa kamar ɗan ƙaramin kwanon sha. Matan Fulani ma na amfani da shi wajen auna nono.

15. Jallo; Ɗan goran duma da ake zuba ruwa idan za a yi tafiya.

16. Shantu; Wani abu ne dangin ƙwarya, tsawonsa kamar tsawon hannu, daga yatsu zuwa kafaɗa, sai dai bai kai kaurin hannu ba. Ana yanke kowane ƙarshe nasa, a rarake cikinsa, kamar dai ɗan guntun fayil na ruwa. Mata na amfani da shi wajen rera waƙoƙi. Su na buga shi a kan cinya su kuma riƙa kaɗa shi da ƴan yatsun hannu, musamman idan an sa zobba ga yatsun, sai ya dinga ba da sautuka masu daɗi kamar ana kaɗa ƙwarya.

17. Jaura; Lokacin da ya fi kowane lokaci sanyi yayin sanyin hunturu.

18. Kindai; Ɗan ƙaramin kwando na Kaba mai marfi, wadda mata ke ajiya a ciki.

19. Farsa; Ɗaya daga cikin sunayen goro kamar daushe, gandi dss.

20. Albada; Sautu ko saƙo.

21. Ƴar shara; Rigar da Bahaushe ya fara ƙirƙira. Riga ce mara hannaye.

22. Kurtu; Kamar ƴar kwalba ko ɗan gwangwani ke nan a halin yanzu, amma wannan na Duma ne. Yawanci ana zuba tawadar rubutu a ciki. Haka tsoffi kan ajiye shi a cikin ɗaki domin zuba yawu. Har a wasu masallatai ma a kan ajiye shi domin zub da yawu.

23. Ala; Baki ya yi ja idan an tauna goro ba a haɗiye ba.

24. Ruɗa-kuyangi; Rana ta yi ja za ta faɗi.

25. Kwiɓin bazawara; Ƴar siririyar hanyar ƙauye, musamman wadda ake tafiya da ƙafa, takan ɗan yi zurfi kuma ciyawa kan fito gefe da gefe. To gefen hanyar ita ce kwiɓin bazawara, wadda idan mai keke ko mai babur ya kuskure tsakiyar hanyar ya taka gefe, santsin ciyawar zai iya kayar da abin hawansa.

26. Mayani; Ƙyalle ko tsumma da tsoffi ke ƙulle wani abu a ciki.

27. Tsariya; Ƙarƙashin gado, musamman irin gadon dauri da akan yi na ƙasa sai a yi ƴar ƙofa daga ƙasa wadda ake sa wuta lokacin sanyi, sai gadon ya yi ɗumi a ji daɗin kwanciya. Yanzu da babu irin wancan gadon, ƙarƙashin kowane irin gado ana iya kiransa tsariyar gado.

28. Asabari; Kamar labulen ƙofa ne da ake yi da siraran kara ko gamba ko wani abu daban. Ana saka shi daga wajen ƙofa, yawanci domin kare feshin ruwa ko rana.

29. Hirji: Addu'a ko neman kariya daga wani abin da ake tsoro.

30. Amaryar wata; Sabon wata, kwanakin farko na wata.

Ƙarin bayani: In da aka ga kuskure, gyara ko ƙarin bayani, ƙofarmu a buɗe take. Mun gode.

Taskar Nasaba

Post a Comment

0 Comments