Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Iya Saduwa Da Mace Mai Haila Idan Na Sanya Condom?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Idan Mace Tana Cikin Haila, Shin Ya halatta Mijinta Yayi Amfani Da Condom Yasadu Da Ita?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To ɗan’uwa bai halatta ka sadu da mai haila ba ko da kuwa ka sanya Condum. saboda Allah Ya haramta saduwa da mai haila, kuma ya kira jinin haila a aya ta 222 a suratul Bakara da kazanta

وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ ۖ قُلْ هُوَ أَذًى فَاعْتَزِلُوا النِّسَاءَ فِي الْمَحِيضِ ۖ وَلَا تَقْرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطْهُرْنَ ۖ فَإِذَا تَطَهَّرْنَ فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ اللَّهُ ۚ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ التَّوَّابِينَ وَيُحِبُّ الْمُتَطَهِّرِينَ ٢٢٢۝

Kuma suna tambayar ka game da haila Ka ce: Shi cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakewa. (Suratul Bakara: 222)

Ba namiji ne kaɗai haila take iya cutarwa ba, idan ana saduwa da mace mai haila mahaifarta za ta takure sai jini ya barke mata, wannan sai yake nuna cewa: ba za’a sadu da mace mai haila ba ko da an sa Condum .

Imamu Suyidi rahimahullah ya ce: ( Babu ban-banci tsakanin saduwa da condom da saduwa batareda condom ba) Ish-tibah wannaza-ir ( 458).

Malamai sun Nassanta haramcin saduwa damai haila koda da condom ne.

Ya zo acikin Tuhfatul- Muhtaaj ( 1/390)

Haramunne saduwa damai haila koda da condom ne. Babu saɓani tsakanin malamai wajan nassohinsu akan haramcin saduwa damai haila koda da condom ne.

Bai halatta saduwa da mai haila ba, da condom ne ko bada shiba, wajibine akan duk wanda ya aikata hakan yatuba yanemi gafarar Allah, da kulla niyyar bazai sake aikata hakan ba.

Bai halatta ga mace ta amsawa mijinta idan yanemi hakan agareta, Idan yaci gaba daneman saduwa da ita tana haila tana da hakkin tanemi saki awajan Alkali, Babu biyayya ga abun halitta wajan saɓon mahalicci.

Dan haka dai babu ban-banci wajan saduwa da mai haila da condom kobada condom ba wajan haramci, haka haramunne mace ta amsawa mijinta akan wannan, Allah yatsaremu dakoyi da yahudawa wajan nunawa Allah wayo cikin Abunda ya haramta musu.

WALLAHU A’ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

ƘARIN BAYANI

Hukuncin Saduwa da Mace Mai Haila ko da da Condom ne

A cikin Qur’ani, Allah ya ce a Suratul Baqara: 222 cewa:

“…ku nisanci mata a lokacin haila, kada ku kusance su har sai sun tsarkake…”

Kalmar “kada ku kusance su” tana nufin haramcin jima’i a farji lokacin haila — ko da an sanya condom — domin abin da aka haramta ba wai jini ne kai tsaye ba, inda ake saduwar ne.

Saboda haka:

Ana iya yin abin sha’awa a sauran sassan jiki fiye da farji, kamar Annabi ya yi wa Matan sa, idan an nisanci farji.

Amma saduwa ta farji lokacin haila haramun ce — da condom ko babu condom.

Idan ya faru…

To wajibi ne a tuba da neman gafarar Allah

Nawafil don gyaran lamari

Ƙuduri ba za a sake yin hakan ba

Babu Laifi ga mace ta ƙi yarda

Mace ba ta da laifi ta ƙi ba, domin ba a yi wa mahalicci sabo saboda halitta. Annabi ya ce:

Babu biyayya ga wani cikin sabo ga Allah.”

Idan miji ya nace, malamai sun ce ta iya kai ƙara ga alkali.

Me ya halatta?

Halal:

Sumbata

Runguma

Abin sha’awa ba tare da kusantar farji ba

Haram:

Ko da an sanya condom

Ko da jinin ya yi ƙasa har sai ta yi wanka (ghusl) bayan haila

Taƙaitawa

Hukunci:

Saduwa ta farji da mai haila haramun ce, kuma condom ba ya canza hukuncin.

Dalili:

Umurnin Qur’ani na nesa da farji a lokacin haila.

Post a Comment

0 Comments