Ticker

6/recent/ticker-posts

Aure A Watan Ramadan

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

assalamun alaikum, gafarta malam ina da tambaya, shin wai akwai wani nassi da ya ce babu kyau ayi aure a watan ramadan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus salam Warahmatulah wabarkatuh.

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah.

 To babu wani abu a Musulunci da ke nuni da cewa haramun ne ayi aure a watan Ramadan, ko saboda wai watan Ramadan ne, ko kuma a wani wata. Don haka, musulunci ya halatta yin aure a kowace rana ta shekara.

 Amma mai azumin ramadana dole ne ya nisanci ci da sha da saduwa tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana. Don haka idan har zai iya kame kansa kuma ba a tsoron ya aikata abin da zai karya azuminsa, to babu laifi ya yi aure a Ramadan.

 Da alama kamar yadda muka sani masu sababbin aure a watan ramadan yawancin su ba za su iya yin hakuri da nisantar matansu ba a tsawon yini, kuma akwai tsoron kada su aikata wani abu da aka haramta kuma su fada cikin zunubi mai girma, wanda akan hakan. wajibi ne a rama azumin ranar tare da kaffara mai tsanani, wanda yake kodai a ‘yanta bawa; idan baza'a iya hakan ba to sai su yi azumin wata biyu a jere; idan kuma hakan shima ba zai yiwu ba to sai su ciyar da miskinai sittin (kamar yadda shari'a ta yi bayani). Idan kuma suka sake yin wani jima'i a cikin kwanaki ramadan ɗin, to dole ne su sake maimaita wannan kaffarar. Ma'ana, idan suka yi jima'i sau 2 ko 3 to zasu yi kaffarar 'yanta bawa 2 ko 3, ko azumin wata 4 ko 6 a jere, ko su ciyar da miskinai 120 ko 240 da sharadin idan ba za su iya na farko da na biyu ba.

 Shawararmu ga wannan mai tambaya ita ce, idan akwai tsoron ba zai iya kame kansa ba, to ya jinkirta aurensa har sai bayan Ramadan, ya shagaltar da kansa a cikin Ramadan, da ibada, karatun Alkur’ani, addu’a. qiyamul layl, da sauran ibadu.

 WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments