Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Saduwa Da Mai Haila

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Idan mutum ya sadu da matarsa tana haila, me ya kamata yayi? kuma ina neman cikakken bayani malam.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. Wanda ya sadu da matarsa tana haila, ya wajaba yayi istigfari saboda ya aikata abin da Allah ya hana a aya ta (222) a Suratul Baqara

وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ قُلْ هُوَ أَذًى فَاعْتَزِلُوا النِّسَاءَ فِي الْمَحِيضِ وَلَا تَقْرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطْهُرْنَ فَإِذَا تَطَهَّرْنَ فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ اللَّهُ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ التَّوَّابِينَ وَيُحِبُّ الْمُتَطَهِّرِينَ

Kuma suna tambayar ka game da haila Ka ce: Shi cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakwa. (Suratul Bakara aya ta 222)

wannan ita ce maganar mafi yawan malamai. Kamar yadda Ibnu Rushd ya faɗa a Bidayatul mujtahid, hadisin da ya zo cewa: (Wanda ya sadu da matarsa tana haila yayi sadaka da rabin dinare) bai inganta ba, wannan yasa ba za'a iya gina hukunci akansa ba.

Allah ne mafi sani.

Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

HUKUNCIN SADUWA CIKIN HAILA BISA RASHIN SANI

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam barka da asubah inatambaya Ni ce ban san jini haila ya zo mun ba mukayi mu'amala da mijina amma bansan ina jini ba saida Nazo tsarki yahukuncina yake?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To Baiwar Allah Matukar dai baki san cewa jinin hailan ya zo ba wato dake da majin duk baku san cewa hailan ya zo ba sai bayan gama mu'amalar auren kikaga hailan to wannan baku da laifi in sha Allahu. Amma idan kin san cewa kina haila aka yi saduwar ko kuma ana cikin saduwar hailan tazo Amma bakuyi maza kun dakata da saduwar ba kawai kuka cigaba a hakan to wannan kuma kuna da laifi Domin Allah madaukakin sarki ya hana saduwa a halin haila Har tsinuwa ya ajiye ga duk me saduwa da mace yayinda take haila.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments