Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Iya Ci Gaba Da Zaman Aure Da Mashayin Giya?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Mijina mutum ne mai shaye-shaye kuma Allah ya azurtamu da haihuwar yara huɗu, don Allah meye hukuncin zamana da shi a addini, shin babu laifi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. Kiyi ƙoƙari wajan yi masa nasiha, Allah zai iya shiryar da shi, in har kina son shi za ki iya cigaba da zama da shi. Wanda yake shan giya fasiki ne, saboda yana aikata babban zunubi, saidai a musulunci tunda zunubin da yake aikatawa bai kai kafirci ba, ya halatta ki cigaba da zaman aure da shi mutukar kina ƙaunar shi.

Allah madaukakin Sarki ya shar'anta saki saboda tunkude cutarwa daga ma'aurata, matuƙar ba zaki iya tsayawa da hakkokinsa ba ya halatta ku rabu, tare da cewa duba makomar yaranku yana da muhimmanci.

Allah ne mafi sani.

Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments