Ticker

6/recent/ticker-posts

Mace Za Ta Iya Aske Gashin Kanta?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Malam gashin matata ne yake karyewa, musamman in tazo tajewa dayawa yana fita. Shine tace tana son ta aske don sabo ya fito.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. Ya haramta ga mace ta aske gashin kanta saboda hadisin da Tirmizi ya rawaito cewa: "Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) ya hana mace ta aske gashin kanta". Idan mace ta aske gashin kanta zai zama ta yi kama da maza, Allah kuma ya la'anci macen da take kamanceceniya da maza kamar yadda ya tabbata daga Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam). Wasu malamai sun halattawa mace ta aske gashin kanta don wani sabon gashin ya fito idan wata lalura ta same ta kamar kora ko ƙwaƙuyewar kai, Ibnu Uthaimin ya ambata hakan a Fataawaa Nurun aladdarb 10/13, sannan, Athram ya hakaito kwatankwacin wannan Fatawar daga Imamu Ahmad.

Allah ne mafi sani.

Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GUq2GCCzlcdL6nknqLYYox

𝐅𝐀𝐂𝐄��𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments