Ticker

6/recent/ticker-posts

Yarjejeniya A Kan Zina

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Ya nemi alfasha da ita, ta ce sai ya biya ta. Ya ba ta dubu goma. Amma ta ki yarda su haɗu kuma ta kashe kuɗin, ina hukuncin haka?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Tun farko dai, bai halatta mace ta keɓance ko ta kaɗaita da wanda ba muharraminta ba, har kuma ta yi magana da shi a kan irin wannan mummunan al’amarin ba. Domin hanya ce mai kusantarwa ga aikata zina wannan kuma haram ne. Allaah Ta’aala ya ce

وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلً

Kuma kar ku kusanci zina. Haƙiƙa ita alfasha ce, kuma mummunar hanya ce. (Surah Al-Israa: 32).

Sannan kuma kamar yadda malamai suka nuna, wannan yarjejeniya ce ɓatacciya a kan ɓarna. Bai halatta a ƙulla shi a tsakaninta da shi ba. domin yarjejeniya a kan zina haram ne kuma abin da aka bayar ko aka karɓa da wannan manufar duk haram ne. Ya tabbata a cikin hadisin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« ثَمَنُ الْكَلْبِ خَبِيثٌ وَمَهْرُ الْبَغِىِّ خَبِيثٌ وَكَسْبُ الْحَجَّامِ خَبِيثٌ »

Kuɗin kare ƙazanta ne, kuma kuɗin karuwa ƙazanta ne, kuma kuɗin mai yin ƙaho ma ƙazanta ne. (Sahih Muslim: 1568).

Wannan kuɗi da ta ci zai iya shiga cikin maganar Ubangiji Tabaaraka Wa Ta’aala cewa

يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَأْكُلُوا أَمْوَالَكُمْ بَيْنَكُمْ بِالْبَاطِلِ

Ya ku waɗanda suka yi imani! Kar ku ci dukiyoyinku a tsakaninku da ɓarna. (Surah An-Nisaa’: 29).

Kuma kuɗin haƙƙi ne da ba nata ba, kuma amana ce a wuyarta da ya wajaba ta sauke kafin zuwa ranar tsayuwa a gaban Ubangijin Halittu. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« لَتُؤَدُّنَّ الْحُقُوقَ إِلَى أَهْلِهَا يَوْمَ الْقِيَامَةِ »

Lallai za a mayar da haƙoƙƙi ga masu su a ranar ƙiyama. (Sahih Muslim: 2582).

Don haka lallai ta mayar masa da kuɗinsa, kuma ta tuba ga Allaah da sharuɗɗan tuban na yin nadama a kan aikata wannan abin, tare da ƙulla aniya mai ƙarfi cewa ba za ta sake aikata irin wannan ko ma wani zunubi ba a iya tsawon rayuwarta. Sannan kuma ta yawaita neman gafarar Allaah a kan abin da ta gabata.

Allaah Ta’aala nake roƙo ya gafarta mata, kuma ya gyara zuciyarta, kuma ya tsare mata matuncinta daga alfasha.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments