Ticker

6/recent/ticker-posts

Wurin Sallar Mata A Jumma’a

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Idan cikin masallaci ya cika maza ne ya kamata su fita zuwa haraba ko mata?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

A asali dai zuwa Jumma’a ba wajibi ba ne a kan mata, kamar yadda hadisi sahihi ya nuna. Haka ma zuwansu sallar jam’i a masallaci tare da maza ba dole ba ne. An hana su zuwa masallacin idan sun nemi izinin hakan, sai dai kuma su yi sallah a gida ya fi alkhairi gare su. (Sahih Abi-Daawud: 567).

A wani lafazin kuma ya ce

« وَلَكِنْ لِيَخْرُجْنَ وَهُنَّ تَفِلاَتٌ »

Amma su fita ba da kwalliya ba. (Sahih Abi-Daawud: 565)

Kuma ya tabbata a cikin hadisin Sahabiya Umm-Humaid matar auren Abu-Humaid As-Saa’idiy (Radiyal Laahu Anhumaa) cewa, ita ce ta je wurin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ta bayyana ma sa cewa tana son yin sallah a tare da shi a masallacinsa? Sai ya amsa ya ce

« قَدْ عَلِمْتُ أَنَّكِ تُحِبِّينَ الصَّلاَةَ مَعِى وَصَلاَتُكِ فِى بَيْتِكِ خَيْرٌ لَكِ مِنْ صَلاَتِكِ فِى حُجْرَتِكِ وَصَلاَتُكِ فِى حُجْرَتِكِ خَيْرٌ مِنْ صَلاَتِكِ فِى دَارِكِ وَصَلاَتُكِ فِى دَارِكِ خَيْرٌ لَكِ مِنْ صَلاَتِكِ فِى مَسْجِدِ قَوْمِكِ وَصَلاَتُكِ فِى مَسْجِدِ قَوْمِكِ خَيْرٌ لَكِ مِنْ صَلاَتِكِ فِى مَسْجِدِى ». - قَالَ - فَأَمَرَتْ فَبُنِىَ لَهَا مَسْجِدٌ فِى أَقْصَى شَىْءٍ مِنْ بَيْتِهَا وَأَظْلَمِهِ فَكَانَتْ تُصَلِّى فِيهِ حَتَّى لَقِيَتِ اللَّهَ عَزَّ وَجَلَّ.

Haƙiƙa! Na san kina son yin sallah tare da ni. Amma kuma sallarki a uwar-ɗakanki shi ya fi sallarki a falonki. Kuma yin sallarki a falonki ya fi sallarki a cikin gidanki. Kuma sallarki a gidanki ya fi sallarki a masallacin unguwarku. Kuma sallarki a masallacin umguwarku ta fi sallarki a masallacina. A kan haka sai ta sa aka gyara mata wurin sallah a mafi ƙuryar ɗakinta a wurin da ya fi duhu. A nan ta riƙa yin sallah har zuwa rasuwarta. (Hadisi Hasan a cikin Al-Musnad: 27090).

Kuma idan mata suka zo masallacin, to sahunsu a bayan sahun maza ya ke, saboda maganarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

« خَيْرُ صُفُوفِ الرِّجَالِ أَوَّلُهَا وَشَرُّهَا آخِرُهَا وَخَيْرُ صُفُوفِ النِّسَاءِ آخِرُهَا وَشَرُّهَا أَوَّلُهَا ».

Mafi alkhairin sahun maza shi ne na-farkonsu, mafi sharrinsu kuma na-ƙarshensu. Kuma mafi alkhairin sahun mata na-ƙarshensu, mafi sharrinsu kuma na-farkonsu. (Sahih Muslim: 440).

Daga waɗannan riwayoyin da makamantansu ana fahimtar cewa: Yin sallar mace a cikin gida a keɓance a inda maza ba za su gan ta ba shi ne ya fi alkhairi gare ta, kuma ga sauran al’umma ma.

A ƙarƙashin wannan idan cikin masallaci ya cika, ba mata ne ya kamata su fito zuwa haraba ba. Domin yin sallarsu a haraba ƙara bayyanar da su ne ga maza. Shiyasa gara dai su mazan su fita zuwa harabar, su bar matan a cikin masallacin. Wannan ne ya fi, in sha Allah.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments