Gyaɗa na ɗaya daga cikin nau’o’in abincin Bahaushe da suka danganci ƙwayoyi. Tsironta ba shi da tsayi ko girma, sannan ganyen tsiron ƙanana ne. Takan yi ’ya’ya ne cikin ƙasa. Gyaɗa na da matuƙar tasiri da muhimmanci a cikin abubuwan da Hausawa ke nomawa. Takan fito da ɓawo (kwalfa) wanda sai an ɓare ake tarar da asalin ƙwayar a ciki. Wannan ne ma ya sa Bahaushe ke da daɗaɗɗiyar waƙar gyaɗa kamar haka:
Gyaɗa mai sihiri,
A ɓare a ga ɗaya,
A murje a ga huɗu,
A tauna a ji garɗi.
Duk da cewa akai nau’o’in miya da dama da Bahaushe ke amfani da gyaɗa a matsayin kayan haɗi, a wannan miyar gyaɗar ce ke kasancewa mafi yawa daga
cikin kayan haɗin.
Mahaɗin
Miyar Gyaɗa
Akwai abubuwan da za a tanda idan za a
haɗa miyar gyaɗa. Abubuwan sun haɗa da:
i. Daddawa
ii. Gyaɗa
iii.
Kabewa
iv. Kayan miya
v. Kayan Ƙamshi/ Kayan yaji
vi.
Magi
vii. Mai
viii. Nama ko kifi (idan da hali)
ix. Ruwa
Yadda
Ake Miyar Gyaɗa
Daga farko za a tafasa nama a saka
albasa da magi da gishiri a ciki. Idan ya tafasa a
aje shi gefe. Sannan a daka daddawa da kayan yaji da tafarnuwa a aje gefe ɗaya. Daga nan a jajjaga tarugu da albasa da tumatur da
tattasai. Za a hura wuta a ɗora tukunya a saka man gyaɗa ko man ja tare da albasa. Idan ya soyu, sai a
zuba jajjagen a ciki a yi ta soyawa inda daga baya za a saka daddawa a ciki.
Ita ma idan ta ɗan soyu sai a yi sanwa.
Bayan wannan ya kammala, sai maganar zuba ruwa da kayan ɗanɗano nau’in su magi. Akan sanya kabewa
cikin wannan miyar idan ana buƙata.
Idan miyar ta dafu sosai za a ɗauko gyaɗa a daka ta
sosai ta niƙu sai a zuba a
ciki. Ba a rufe tukunya gaɓa ɗaya
yayin da aka sanya waɗannan abubuwa. A maimakon haka, za a ɗan ɗaga marfin tukunyar ne gudun kada gyaɗar da ke ciki ta yi bori ta zube. Irin wannan nau’in miya akan ci ta da tuwon shinkafa ko masara da makamantansu, wani lokaci ma har ɗanwake ake ci da ita.
Tsokaci
Miyar gyaɗa tana
matuƙar taimaka wa ga mai juna biyu. Wannan
ne ma ya sa ko a asibitoci ake ƙarfafa
yin wannan miya. Ya tabbata cewa takan ƙara wa jiki kuzari. Akan samu ɗaiɗaikun mutane da wannan miya kan samar
wa illa, musamman wanda ya shafi ɓacin ciki. Miya ce da ake yin ta a birni da ƙauye.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.