Egushi yana daga cikin ’ya’yan itace da Hausawa suka samu a yankin kudancin ƙasar nan. Saboda haka ne ma, egushi bai yawaita sosai a ƙasar Hausa ba. Sannan yawanci ba Hausawa ne ke sayar da shi a ƙasar Hausa ba. A dalilin haka, miyar egushi ba ta yawaita a ƙasar Hausa ba.
Mahaɗin
Miyar Egushi
Kayan haɗin
miyar egushi sun haɗa da:
i. Albasa
ii. Egushi
iii. gishiri
iv. Kayan ciki ko nama ko kifi (idan akwai)
v. Kayan yaji
vi. Kori
vii. Magi
viii. Manja ko mangyaɗa
ix. Ruwa[1]
x. Tafarnuwa
xi. Tarugu
xii. Tattasai
xiii. Thyme
xiv.
Tumatur
Yadda
Ake Miyar Egushi
Da farko za a wanke kayan ciki (idan za a yi amfani da su). Za a
sanya musu nau’o’in kayan ɗanɗano
sannan a bar shi har sai ya tsane. Daga nan, za a jajjaga tarugu da tattasai
kar a saka tattasai ya yi yawa sosai. Sannan za a saka ɗan tumatur kaɗan shi ma a jajjaga sama-sama sai a
saka ’yar kanwa kaɗan a ciki a aje. Bayan nan, za a soya
mai tare da albasa a soya jajjaagen. Bayan sun soyu, za a saka
kayan yaji dangin su citta da kanamfari.
Bayan wannan ya samu, za a yi sanwa a saka magi da gishiri
kaɗan. A wannan gaɓa ne kuma za a sanya kayan cikin da aka tanada. Daga nan
za a ɗauko agushi a fece shi tare da cire
dattin da ke tare da shi a
kuma daka. Bayan an kammala daka, sai a kwaɓa
shi. Idan a na buƙata ana iya
saka karas a cikin.
Sai dai dole sai an goge karas an yanka kafin a sanya. Bayan haka, akan sanya
koren tattasai.
Tsokaci
Wannan nau’in miya an fi samun ta a gidajen masu hannu da shuni.
Sannan an fi yin miyar a cikin birane sama da ƙauyuka. Hasali ma, ba kasafai ake samun egusi a
kasuwannin ƙauyuka ba.
[1] Idan an lura, akwai nau’in kayan ɗanɗano na musamman da ake amfani da su
yayin samar da wannan miyar.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.