Ticker

6/recent/ticker-posts

Wane Lokaci Ne Ake Shan Ruwa (Buda Baki)?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum dan Allah tabbaya nake unguwar danake ne ba ajin qiran sallar magariba sakamakon masallacin da dan nisa shi ne nakeso afadamin dai-dai Lokacin shan ruwa (Buɗa baki) Allah qara basira.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis Salaam: Lokacin shan ruwa (buɗa baki) yana tabbata ne da zarar rana ta faɗi. Allah maɗaukakin sarki cewa yayi

 ۖ ثُمَّ أَتِمُّوا الصِّيَامَ إِلَى اللَّيْلِ ۚ

Mu cika azumi izuwa dare kamar yadda aya ta 187 ta cikin suratul Baqara tayi bayani

Shikuma dare yana farawa daga lokacin da rana ta faɗi wannan ita ce fahimtar dukkan malamai. Sabida haka lokacin shan ruwa ga me azumi yana farawa daga sadda rana ta faɗi, kenan matukar dai rana ta faɗi mutum yasha ruwan to azuminsa ya yi in Shã Allahu koda kuwa masallacin da yake kusa dasu basu kira sallah ba.

Ba sharaɗi bane koda rana ta faɗi kuma ace dole sai an kira sallah sannan mutum zaiyi buɗa baki, a'a sharaɗin kawai shi ne faɗuwar ranar.

Abinda Zakiyi Shi ne Ki Tura Mijin Ki Ya Tambaya Muku Shin Karfe Nawa ne Suke Yin Kiran Sallah ko Suke Yin Buɗa-Baƙi a Wannan Unguwan, ko Kuma ki Nemi izini ki je Ki Tambaya Shin Karfe Nawa ne Rana Yake Faɗuwa?

Tunda Ke Ba Jin Kiran Sallah a Masallaci. Idan Ladan Ko Wakilan Masallacin Sun Gaya Miki Lokacin da Rana take Faɗuwa Sai Kiyi Amfani da Agogon Wayar Ki Wajen Yin Buɗa-Baƙin ki. Idan Kuma Hakan Bai yi ba Sai Ki Duba da Kanki Shin Karfe Nawa ne Rana take Faɗuwa? Idan Kin Gani Kin Tabbatar da Time naki Sai Kike Amfani da Lokacin Faɗuwar Rana wajen yin Buɗa-Baƙin ki.

Domin Annabi Muhammad Mai Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Agare Shi, Yana Cewa Ku Jinkirta Yin sahur Ku Gaggauta Yin Buɗa-Baƙi a Lokacin da Rana ta Faɗi. Sabida haka da Zarar Rana ta Faɗi kin Tabbatar da Faɗuwar ta, toh ko ba ki Ji Kiran Sallah na Ladan ba Za kiyi Buɗa-Baƙin ki Kuma Azumin ki Yayi.

Sa'annan Mu Kara Kula da Time Namu, Domin Ana Cikin Damina ne a Wasu Jihohin, Wani Lokacin Zaki ga An Yi Ruwan Sama daga Karfe 5:00pm zuwa 6:00pm Sai Ki ga Gari ya yi Duhu Bayan Ruwa ya Ɗauke ki ɗauka Cewa ai Rana ta Faɗi Magriba ya yi don Haka bari Ki Sha Ruwa Yanzu.

 Idan Kin yi Haka da Ganganci kika Sha a Cikin Rana to Azumin Ki ya Lalace na Wannan Yinin Sannan Zakiyi Kaffara. Idan a Rashin Sani Kika yi Shikenan kin dai Wuni da Yinwa da Kishin Ruwa Saura kan Kiyi Buɗa-Baƙi sai kika Karya Azumin ki, Saboda haka bayan Sallah zaki Rama 1.

Misalin a Garin Ku Ana yin Buɗa-Baƙi Kullum Karfe 5:50pm, Yau Sai Aka Yi Ruwan Sama aka Ɗauke Ruwan Sai Gari ya yi Duhu, Sai irin Karfe 5:30pm kika ce ai Yanzu Rana Ya Faɗi domin ga Duhu Saboda haka bari Kiyi Buɗa-Baƙin ki yanzu bayan Kuma ga Yadda Kika yi Buɗa-Baƙi a jiya Karfe 5:50pm. Toh Kisani Azumin ki ya Lalace Domin Kin Yi Buɗa-Baƙi ne a Cikin Rana, Ranan bata gama Faɗuwa ba ki Yi Buɗa-Baƙin ki.

Sabida Haka Muke Yin Amfani da Time na Agogon Wayar mu Wajen Yin Buɗa-Baƙi koda An Yi Ruwan Sama ne a Lokacin Duhu ya Sauka kada Muyi Gaggawan Yin Buɗa-Baƙi Alhalin Rana bai Faɗi ba.

Duk Wanda ya Kuskura ya yi Buɗa-Baƙi rana bai faɗi ba, Azumin sa ya Lalace. Idan da Ganganci ya yi Sai ya yi Kaffara, idan Kuma a Rashin Sani ne Azumin shi na Yinin Ya ƙarye Bayan Sallah zai Rama 1. Da Ganganci Shi ne Ace Mutum ya ga Irin Wannan Tunatarwan sa'annan ya San cewa Rana ba ta Fadi ba ya Ƙi Amfani da shi ya Bi Son Zuciyar sa. Toh Kaffara zai Kama Shi.

Idan da Rashin Sani Shi ne Ke Ba ki San Lokacin da Rana take Faɗuwa ba sai kika yi Gaggawan Shan Ruwa a Lokacin da kika ga Duhu kuma Alhalin Rana bai Faɗi ba. Toh babu Kaffara a kanki Kawai biyan 1 zakiyi.

Haka Nan a Lokacin Sahur Muke Yin Amfani Lokacin Fitowar Alfijir, idan Yau Alfijir Na Garin Ku Ya Fito Sai ki Duba Karfe Nawa ne? Idan Kin gani Sai Kiyi Amfani da Time ɗin. Saboda Haka Kowa Abinda Yakamata ya yi Kenan ayi Amfani da Time na Agogon Wayar Mu, Ki bada Ratar Minti 30/20 Tsakanin ki da Fitowar Alfijir.

Shi Kuma Shan Ruwa Kuma Rana tana Faɗuwa ko Ladan bai yi Kira ba Ki Gaggauta Yin Buɗa-Baƙin ki.

WALLAHU A'ALAM

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments