Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan Jinin Haila Ya Daukewa Mace Kafin Fitowar Alfijir

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin idan al'adar mace ya ɗauke sai tayi wanka bayan fitowar alfijir, sai tayi sallah ta yi azumi, shin za ta rama azumin wannan ranan??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Idan al'ada ya ɗaukewa mace kafin fitowar alfijir koda da minti ɗaya ne kuma hakan a ramadan ne to ya wajaba akanta tayi azumin wannan ranan, domin tayi azumi tana cikin tsarki, koda kuwa batayi wanka ba sai bayan fitowar alfijir, kamar namiji ne da ya tashi da janaba ajikinsa sawa'un na saduwa ne ko kuma na mafarki, baiyi wanka ba har sai bayan fitowar alfijir azuminsa yana nan babu abinda ya sameshi.

Aƙarƙashin wannan zanso in faɗakar da mata akan wani abu, idan al'ada ta zowa mace bayan faɗuwar rana kafin tayi sallan magriba, azuminta na nan bai ɓaci ba, koda kuwa yazo matane bayan faɗuwar rana da minti ɗaya, azuminta ya cika"

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments