Sahu A Bayan Limamiya

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum. Ina da yara biyu mace mai shekaru 11 da namiji mai shekaru 8. Idan zan yi musu limanci a gida a matsayina na mahaifiyarsu, yaya sahun zai kasance?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

    Da-farko dai a masallaci ya kamata yaro mai shekaru 8 ya riƙa yin sallar farilla a sahun maza. Wannan ya shiga ƙarƙashin umurnin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya bayar ga iyaye cewa

    « مُرُوا أَوْلاَدَكُمْ بِالصَّلاَةِ وَهُمْ أَبْنَاءُ سَبْعِ سِنِينَ وَاضْرِبُوهُمْ عَلَيْهَا وَهُمْ أَبْنَاءُ عَشْرِ سِنِينَ وَفَرِّقُوا بَيْنَهُمْ فِى الْمَضَاجِعِ ».

    Ku umurci ’ya’yanku da yin sallah a halin suna ’yan shekaru bakwai, kuma ku buge su a kan ta a halin suna ’yan shekaru goma, kuma ku rarrabe a tsakaninsu a shimfiɗa. (Sahih Abi-Daawud: 509).

    Malamai sun nuna cewa, kulawa da sharuɗɗan sallar ya shiga cikin wannan umurnin. Don haka koya musu sanin lokaci da tsarki da rufe al’aura da fuskantar alƙibla da daidaita sahu da makamantan hakan duk sun shiga cikin abubuwan da ake koya wa yara a lokacin da suka kai shekaru bakwai.

    Shi kuwa namiji wajibi ne ya yi sallarsa ta farilla tare da jama’a a cikin masallaci saboda dalilai masu yawa da suka haɗa da hadisin makahon nan da ya zo neman sassaucin ko ya samu ya yi sallarsa a gida? Amma kuma bai samu wannan sassaucin daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba. (Sahih Abi-Daawud: 561).

    Don haka wannan ma yana daga cikin abin da ya wajaba a koya wa yara maza ’yan shekaru bakwai-bakwai, kafin su kai shekaru goma lokacin da za a buge su idan ba su kula da su ba.

    Amma idan larura, kamar ta ruwan sama ko rashin lafiya ko matsalar tsaro da makamantan hakan, ta sa yaron zai yi sallah a gida tare da ke da yayarsa, to shi ya kamata ya zama liman idan har zai iya yin limancin. Ke da yayarsa kuma sai ku yi sahu a bayansa. Ya halatta yaro wayayye da bai balaga ba ya yi limanci a maganar da ta fi ƙarfi a wurin malamai, saboda hadisin Amr Bn Salamah (Radiyal Laahu Anhu) wanda yake yi wa mutanen ƙauyensu limanci tun yana ɗan shekaru shida zuwa bakwai, domin shi ne ya fi su karatun Alqur’ani. Hadisin yana cikin Sahih Al-Bukhaariy: 4302.

    Idan kuma ba zai iya limancin ba, to abin da ya fi - a fahimtata - sai ke da yayarsa ku tsaya a sahu guda, limamiyar tana a hagu, shi kuma yaron ya tsaya a hagun limamiyar. Domin ita limamiya da ma a tsakiya take tsayawa, kamar yadda ayyukan sahabbai irin su A’ishah da Ummu-Salamah daga cikin Ummuhaatul-Mu’mineen (Radiyal Laahu Anhunn) ya nuna. Haka Ibn Hazm a cikin Al-Muhallaa: 4/309-311, da Abdurrazzaaq a cikin Al-Musannaf: 3/140-141, da Ad-Daaraqutniy a cikin As-Sunan: 1/404-405 suka riwaito, kuma As-Shaikh Al-Azzaaziy a cikin Tamaamul Minnah: 1/316 ya ce: Sahih Li Ghairih.

    Allaah ya ƙara mana fahimta.

    WALLAHU A'ALAM 

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.