Ticker

6/recent/ticker-posts

Wadanda Suke Yin Azumi Da Wahala, Sai Su Ciyar Da Miskinai

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam dan Allah inada tanbaya. Mace ce tasha azumi na alada kuma bayan haka duk azumi akarshe saitayi ulcer har ba a gama azumi da ita balafiya sannan bayan azumi da wata ɗaya sai tasamu ciki kuma duk ciki saitayi laulayi har bazata iya rama azumi ba, har saita haihu bayan ta haihu kuma ga shayarwa shima takasa rama azumin harda wasu matsalolin rayuwa in tadau azumin wataran zatarasa Abun buda baki, saboda karancin samu mijinta hardai yakai tasha azumi yakai kamar shekara uku kuma yanzu tasamu dan wadatar dazata iya ciyarwa zata iya ciyarwan ko kuwa? kuma agaskiya rama azumin nan zataita rashin lafiya saboda dayawa Kinsha nasa ulcer Dan Allah malam karka shareni.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahamtullahi Wabarkatuh

Indai abinda kika fada kin tabbatarda hakanne to zaki ciyar da miskinai.

Misali: idan ana binki azumi 40 ne, zaki ciyar da miskinai 40.

Zaki iya ciyar dasu lokaci ɗaya dukansu. Ko kuma ki rika ciyar da mutum 1 kullum har ki gama.

Allah yace

... فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ وَعَلَى الَّذِينَ يُطِيقُونَهُ فِدْيَةٌ طَعَامُ مِسْكِين ...

Wanda ya kasance daga cikinku maras lafiya ko kuma yana akan tafiyi, to ya biya (Azumin) da wasu kwanaki na daban (Bayan watan azumi), wadanda suke yinsa (azumin) da wahala akwai fansa (shine su) ciyarda Miskinai..... (Suratul Bakara aya ta 184)

Saidai idan akwai halin yin azumin, to yin azumin yafi. Saboda fadar Allah

وَأَن تَصُومُوا خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ

Kuma kuyi azumi shi yafi alkhairi agareku, idan kun kasance kun sani. (Suratul Bakara aya ta 184)

Saboda haka a yanayin wannan tambaya ta nuna cewa bazaki iya yin azumi ba, saboda haka zaki ciyar da talakawa ne adadin yawan azumin da ake binki.

Haka kuma idan azumin Ramadan yazo zaki ciyar da miskini a kullum saboda yin azumin gareki akwai wahala sosai.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments