Ticker

6/recent/ticker-posts

Hadisin Sanarwar Watan Ramadan

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam menene gaskiya magana akan wannan sakon da ake yaɗawa a social media "Azumin watan Ramadan zai fara Ranar 11-03-2024 insha Allah. Annabi Sallallahu alaihi Wasallam. yace duk Wanda ya sanar da wani labarin zuwan watan ramadan, wuta ta haramta gareshi. Allah yasa mudace"

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahamtullahi Wabarkatuh

Wannan karyce kai tsaye dan babu wata hadisin da Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya faɗi hakan, kai hasalima cewa yayi.

عن ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ - ﻗﺎﻝ : ‏( ﻣﻦ ﻛﺬﺏ ﻋﻠﻲ ﻣﺘﻌﻤﺪﺍ " ﻓﻠﻴﺘﺒﻮﺃ ﻣﻘﻌﺪﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﻨﺎﺭ ‏) . ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ

An karɓo daga Abi Hurairata Yardan Allah ya tabbata agarehi: Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agareshi) yace: Duk wanda yayi karya agareni ya tanadi mazauninsa (masaukinsa) a wuta. Muslim ne ya rawaitoh shi.

Yan uwana MAZA/MATA Dan Allah waƴenda sukasan suna aikata hakan yadai kamata subari dan yin hakan yana nuna rashin biyayyah ga Annabi Sallallahu alaihi Wasallam. Akiyaye.

Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace, Fadi alkhairi koh kayi shuru

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments