Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Azumin Nafila Ga Wanda A Ke Binsa Bashin Farilla

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin ko ya halatta mutum yayi azumin nafila alhali ana binsa bashin azumin farilla bai rama ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Malamai sunyi saɓani dangane da hukuncin yin azumin nafila ga wanda a ke binsa bashin farilla, shin dole ne sai ya fara gabatar da ramuwar wannan farillar sannan ya ke da ikon yin nafila ko kuma a'a zai iya yin nafila daga bisani kuma yayi farillar? An samu maganganun malamai kamar guda uku akan haka

1. Ƙauli na farko shi ne, Mazhabin Hanafiyya da Zahiriyya sun tafi a kan cewa kai tsaye ba tare da wani karhanci ba ya halatta mutum yayi azumin nafila kafin ya rama wanda a ke binsa na ramadan. Dalilinsu na cewa ya halatta shi ne, sukace ba wajibi ba ne ga wanda a ke binsa bashin azumi a ce sai ya ramashi cikin gaggawa, dan haka yana iya jinkirta yin ramuwar azuminsa zuwa wani lokaci na gaba, sannan suka kafa hujja da wannan Hadisi na A'isha matar Mαnzoи Aʟʟαн (Sallallahu alaihi Wasallam) wanda take cewa

"كان يكون علي الصوم من رمضان فما أستطيع أن أقضيه إلا في شعبان"

MA'ANA

Ya kan kasance akwai ramuwar (azumin) ramadan a kaina amma ba na samun ikon rama shi har sai sha'aban ya zo.

Dan haka anan sukace wani lokacin uzuri ya kansa A'isha ta kasa rama azumin da ke kanta har sai watan sha'aban ya zo ta ke ramawa.

Sannan sukace abu ne sananne ga A'isha wajen kwaɗayinta na yin nafiloli, dan haka zeyi wahala a ce wai ba tayin azumin nafila musamman kamar irin su: azumin tasu'a, azumin ashura, azumin ranar arfa, azumin sitta shawwal, da kuma azumin watan zulhijja

2. Ƙauli na biyu shi ne, Mazhabin Malikiyyj da Shafi'iyya sun tafi a kan cewa makaruhi ne a kan wanda a ke binsa bashin azumin farilla kuma yace zeyi na nafila. Dalilinsu kuwa shi ne, sukace mutum ya fara biyan bashin da a ke binsa na azumi shi ne yafi muhimmanci a gare shi a kan ya shagaltu da yin azumin nafila, dan haka sukace makaruhi ne.

3. Ƙauli na uku shi ne, Mazhabin Hanabila an samu ƙauli guda biyu a wajensu, akwai ƙaulin da sukace ya halatta sannan akwai ƙaulin da sukace haramun ne mutum yayi azumin nafila dole sai in ya fara rama wanda a ke binsa bashi tukuna, daga cikin dalilansu na cewa haramun ne sun kafa hujja da wannan hadisi ko da yake wasu Malamai sunce hadisin bai inganta ba

"………ومن صام تطوعا وعليه من رمضان شيء لم يقضه لم يتقبل منه"

MA'ANA

………Wanda yayi azumin nafila alhali akwai wani abu na ramadan a kansa da bai rama ba to ba za a karɓa masa (azumin nafilar da yayi ba)

To amma magana mafi inganci kamar yadda mafi yawan Malamai suka rinjayar itace, ya halatta mutum yayi azumin nafila musamman azumin da a ka iyakanceshi da wasu raneku na musamman kamar azumin ranar arfa da sauransu, wanda idan lokacinsu ya wuce shikenan sun kuɓucewa mutum, to a nan ya halatta mutum yayi wannan azumin ko da kuwa ana binsa bashin na farilla da bai rama ba, sai dai duk da cewa ya halatta ayi to amma abu mafi kyau shi ne an fi son mutum ya gaggauta biyan bashin da a ke binsa na farilla.

Amma idan ya kasance azumin sitta shawwal ne Malamai sukace mutum ba zai yi ba har sai in ya fara rama wanda a ke binsa na ramadan tukuna, domin wanda ya cika azumin ramadan to shi ne idan yayi azumin sitta shawwal za a bashi ladan kamar yayi azumin shekara, dan haka sai Malamai sukace wanda a ke binsa ramuwar azumi to ko da yayi azumin sitta shawwal ba shi da lada domin shi bai kammala azumin ramadan ba.

шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

      Mυѕтαρнα Uѕмαи

       08032531505

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments