Ticker

6/recent/ticker-posts

Tuwon Dusa

Wannan nau’in abinci ne da ake sarrafa dusa domin samar da tuwo. Za a tara dusa adadin yadda za ta isa a yi tuwo da ita. Kenan dai ba dusar kwana ɗaya za a yi tuwo da ita ba sai ta kwana biyu ko uku. Idan kuwa ta rana ɗaya ake buƙatar yin tuwo da ita, za a yi karo-karo ne a ba wa mutum guda don ya tuƙa tuwon dusar. Tuwon dusa dai ba kullum ake yin sa ba a gidan Bahaushe. Ana ɗaukar lokaci mai tsawo kafin a tuƙa shi. Abinci ne na gargajiya da ake gudanar da shi a ƙasar Hausa.

Mahaɗin Tuwon Dusa

i. Dawa ko Gero 

ii. Ruwa

Da farko, mutanen yankin Kabi na kiran wannan nau’in tuwo da ƙudu-ƙuduri. Idan za a yi shi, dusa za a samo ta dawa ko gero a zuba ta a turmi a yi ta dakawa sai ta yi laushi ta zama gari. Daga nan sai a mulmula ta kamar yadda ake mulmula dawo in za a sanya shi cikin tukunya. Da zarar an kammala, sai batun kunna wuta tare da aza tukunya da ruwa.

Bayan ruwan ya yi zafi sosai, za a ɗauko dunƙulan na dusa a sanya cikin tukunya kamar dawo. Za a bar shi nan cikin tukunya har sai ya nuna. Da zarar ya nuna yadda ya kamata, sai batun fitarwa tare kuma da sanya miya domin ci. Shi ma tuwon dusa an fi haɗa shi da miyar kwaɓe ko sansamin kuka.

Tsokaci

Shi ma tuwon dusa akasari mata da yara ƙanana ne ke yawan cin sa a yankunan ƙauyuka da garuruwan ƙasar Hausa. Da wuya a samu masu cin tuwon dusa daga cikin mutanen birni, hasali ma wasu ba su san yadda ake yin sa ba. Bayan wannan, a ƙasar Hausa ba kowane gari ake yin tuwon dusa ba. An fi yin sa a garuruwan Kabi da Sakkwato da Zamfara. Ba a cika yin tuwon a garuruwan Zazzau da Katsina da Kano da sauran garuruwan ƙasar Hausa ba. Tuwon dusa cin sa yana da amfani sosai musamman ga maza da mata saboda yana daga cikin abincin da ke ƙara wa jikin mutum ƙarfi da kuzari. Masana kimiyyar abinci sun tabbatar da alfanun abincin da aka yi da dusarsa ga lafiyar jiki tare da kariya ga cututtuka irin na suga (Diabetes) da dangoginsu. Kenan tuwon dusa ba mata da yara kaɗai ya kammata su riƙa cin sa ba, har da maza manya. Sai dai yana da kyau a kula sosai, tare kuma da kauce wa amfani da dusar da ta daɗe a ajiye. A koyaushe a riƙa amfani da saburwar dusa. 

The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology. Data is collected from interviews with different categories of people including: i.          Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets. ii.         People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas. iii.        Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets. Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas. The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.). Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes. Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food. 7th November 2022
Citation: Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments