Tuwon ƙullu, tuwo ne da ake tuƙawa idan an niƙa gero ko dawa da kuma masara a haɗe wuri guda. Wannan garin gero da na masara ake sarrafawa a matsayin ƙullu tare da mayar da shi tuwo. Tuwon kullu na da daga cikin abincin gargajiya da kusan Bahaushen birni da ƙauye ke amfani da shi. Abinci ne da ba shi da nauyi a ciki. A koyaushe za a iya cin tuwon ƙulu a lokutan dare da rana da kuma safiya. Har a lokutan bukukuwa Bahaushe na tanadar tuwon ƙullu. Akasarin mutane ba su cika son cin tuwo wanda ke sa nauyi a cikinsu ba.
Mahaɗin
Tuwon Ƙullu
i.
Masara da Gero ko Dawa
ii.
Rogo
iii.
Ruwa
Yayin samar da tuwon ƙullu,
akan tanadi masara tare
da gero ko dawa. Za a surfe su a cire
dusar a kuma wanke su. Daga nan za a jiƙa ya kwana a jiƙe. Washe gari za a wanke jiƙaƙƙen
surfen da aka yi sannan a niƙa
da dutse. Da zarar an kammala gurzawa, za a dama shi da hannu, sannan a ƙara masa ruwa a kuma tace. Bayan an
kammala tacewa, za a bar shi ajiye har sai ruwan ya kwanta.
A ɓangare guda kuma, za a hura wuta a aza tukunya tare da ruwa. Bayan ruwan ya tafasa, za a kawo
wannan ƙullu,
a ɗan ƙara masa ruwa kaɗan, sannan a zuba cikin wannan ruwa da
ya tafasa. Daga nan za a ɗauko muciya a yi ta tuƙi a hankali har sai ya yi kauri ya
zama tuwo. Lokacin za a ɗauko garin rogo niƙaƙƙe
a zuba ciki a haɗa a tuƙe. Idan ya tuƙu,
za a lura da shi sosai ka
da ya yi kauri ko ruwa-ruwa sama da yadda ya kamata
ya yi. Haka ma, kar a
bari ya yi ƙolalai. Za a
iya ƙara ruwan zafi a ƙara
tuƙawa idan an fahimci buƙatar hakan. Bayan an kammala, sai a ɗan zuba ruwan zafi a rufe tukunyar. Idan ya ƙara dafuwa sai a ƙara tuƙawa sannan a kwashe. Miyar yauƙi
ta fi daɗin sha’ani dangane da cin wannan
nau’in tuwon.
Tuwon ƙullu
maza da mata da yara suna cin sa. Sai dai tsofi sun fi cin sa fiye da mata da
maza. Hakan na faruwa ne kasancewar tuwon ƙullu
mai taushi da ruwa-ruwa. Yayin da aka ci wannan abinci, ciki ba zai yi nauyi ba. Wannan ya sa za a iya
cin tuwon ƙulu mai yawa ba tare da an san an ci shi da yawa
kamar sauran nau’o’in tuwo ba. A garuruwan Kabi da Zamfara da Katsina da Sakkwato an fi yin tuwon ƙullu saɓanin
sauran garuruwa irin su Bauchi da Kano da sauran su. Yana da kyau a ƙara farfaɗo da yin tuwon ƙullu musamman saboda irin tagomashin da ya ke da shi ga
tsofafinmu na ƙasar
Hausa waɗanda
ba sa
iya cin nau’o’in
abincin
zammani a sakamakon nisan da
shekarunsu suka yi, kuma sannan ba kowane abinci ne cikinsu ke iya ɗauka
ba. Haka kuma, tuwon ƙullu yana da sauƙin taunawa a wurinsu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.