𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Malam dan Allh
inada tambaya: Menene hukuncin auren da Al'ada da Taklifi (Tsanantawa) suka
mamaye shi a Sharia?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa rahmatullahi
wa barakatuhu.
Irin wannan auren ba za'a ce bai
yiwu ba. Sai dai ace masu yinsa sun kauce ma tsari irin na sunnar Manzon Rahama
(Sallallahu alaihi Wasallam).
Shaikh Dr Muhammad Bakru Isma'eel
acikin littafinsa mai suna Fiqhus Sunnah, juzu'i na biyu shafi na 37 yana cewa "Duk
da cewar shari'ah mai hikima (wato shari'ar musulunci) bata ajiye wani iyaka
game da Qankantar sadaqi ko Qurewar yawansa ba, to amma ba'a son zurfafawa
acikinsa saboda cikin yin hakan akwai tsanantawa da takurawa. Domin tsanantawa
cikin sadaqi (ko dukiyar aure) shike sanya samari suna kauda kansu daga yin
aure, kuma wannan shi ke haifar da abubuwan ɓarna
waɗanda ba boyayyu
ba, game da lalacewar dabi'a da zamantakewar jama'a".
Duk da cewar shi Malamin yana
magana ne kaɗai game
da tsadar sadaqi, to amma mu anan Qasar hausa bayan tsadar sadaqin ma akwai
wasu miyagun bidi'o'in da mutane suka Qirkiro suka ɗora ma kansu, waɗanda harma anfi tsanantawa akansu fiye da
shi kansa sadaqin ma.
Daga cikin abubuwan da zan iya
tunawa ana yinsu anan Qasar hausa game da bidi'o'in aure akwai
1. Kayan
"Na-gani-inaso".
2. Kuɗin Tambayar arziki.
3. Kayan Sa-rana.
4. Kuɗin Mijin-baya (wanda ake bama 'ya'yan kawunnan
amaryar).
5. Kudin rigar waliyyi.
6. Kuɗin Uwar Amarya.
7. Kuɗin Sa-lallen Amarya.
8. Sa lallen Ango.
9. Party, Picnic, etc.
10. Fulani day.
11. Kauyawa day.
12. Arabian Night.
13. Rawar kalangu.
14. Cakuduwar Maza da Mata.
15. Kuɗin sayen bakin amarya.
Waɗannan
kaɗan ne na zakulo.
Koda ba'a yin wasu daga cikinsu ayankin da kake rayuwa, to awasu yankunan duk
ana yi, ko fiye da haka ma.
Waɗannan
abubuwan duk sun saɓa
ma sunnar Annabi Muhammadu (Sallallahu alaihi Wasallam), wanda Shi Allah ya
aiko mana kuma yace mu kwaikwayi aikinsa. Tabbas hakika Manzon Allah
(Sallallahu alaihi Wasallam) yayi aurarraki da dama, kuma shima ya aurar da
dukkan 'ya'yansa mata. Amma ba'a ruwaito cewa an taɓa aikata koda guda ɗaya cikin Waɗannan
abubuwan alokacin bikinsu ba.
Lokacin da ya auri Nana A'isha
wasu mata ne 'yan tsiraru suka rakota, kuma ba'a yi wani biki ko kade-kade ba,
ballantana cakudar maza da mata. Haka kuma lokacin da ya aurar da 'yarsa
Fatimah wacce ita ce Shugabar dukkan matayen duniya da lahira amma ba'a yi biki
ko rawa ko shagali ba.
Imamu Ahmad bn Hanbal ya karbo ta
hanyar Nana A'isha (Allah ya yarda da ita) tace Manzon Allah (Sallallahu alaihi
Wasallam) yace "Hakika auren da yafi albarka shine wanda dawainiyarsa tafi
sauki"
Awani hadisin kuma yace "Albarkar
mace shine : Saukin sadaqinta, da saukin dawainiyar aurenta, da kyawun
halayenta.
"Shu'umancin mace kuma yana
cikin : Tsadar sadaqinta, Wuyar dawainiyar aurenta, da kuma munin halinta"
Shaikh Muhammad Bakru Isma'eel
yace "Da yawa daga cikin mutane sun jahilci wannan sanarwar ta Manzon
Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) shi yasa suke kauce mata suke bin hanyoyi
irin na zamanin jahiliyyah cikin zurfafa sadaqi (ko dawainiyar aure) suna la'akari
da Qarairayin abubuwa bayyanannu.
Sai kaga mutum yana Qin aurar da
'yarsa ga wani mutum komai matsayin ilimin mutumin ko mutuncinsa ko rikon
addininsa. Sai dai (in sunga alamar cewa) mutumin zai iya biyan sadaqi mai
yawa, basu damu da halin mutumin ba.... Sai kace ita yarinyar da za'a aurar ɗin ta zama wata kadara ce
za'a saye ko sayarwa".
Shehu Usmanu ɗan Fodio acikin
littafinsa IHYA'US SUNNAH (shafi na 123) da yazo yin bayanin bidi'o'in shaiɗanci da mutane suka
kirkiro acikin lamarin aure sai yace "Yana daga cikin wannan (bidi'o'in)
irin bikin walimar dake haɗe
da Ɓarna
kala-kala (kamar chashe rawa ko chudanyar maza da mata) wannan bidi'ah ce
muharramah bisa ra'ayin dukkan malamai.
Shehu yace "yazo acikin
sharhin ALMUFIDAH : Babu kokwanto cikin haramcin wannan da kuma muninsa".
Muna neman tsarin Allah daga ɓacewa
da taɓewa.
Yaci gaba da cewa "Zaka ga
mutum (Allah ka tsaremu da saɓonka
da rashin kishin iyali) kaga mutum wai farkon abinda zai buɗe dashi cikin aurensa
kuma ya gina auren nasa akai shine wannan fasadin mai girma. Wanda duk mutum
dake da kwayar zarrah na kishin musulunci bazai yarda da haka ba. Balle kuma
wanda keda rikon addini koda Qankani ne.
Zaka ga mutum ya tara jama'a ya
girmamasu (wato ya basu wuraren zama da abinci) sannan mataye daga dangin Mijin
suyi ado suyi kwalliya su fito su haɗu
da Waɗannan jama'ar
da ya tara, sannan mutane su tattaru daga kowacce nahiya".
Sannan yace "Babu shakka duk
bikin auren da ya zamto bisa wannan tsarin aka yishi, to babu albarka cikinsa
kuma babu alkhairi. Kaicon shi kansa Mijin (wato angon) da kuma duk waɗanda suka taimaka masa
wajen shirya wannan shu'umin taron koda da garwashin wutar kunnawa ne".
Anan nake jan hankalin matasa
cewar kuji tsoron Allah ku kiyayi aikata irin waɗannan
miyagun bidi'o'in idan kun tashin yin aure. Sannan iyaye ma ya zama wajibi ku
sanya ido ku rika yin nasiha ga 'ya'yanku game da irin waɗannan haramtattun
bidi'o'in, mutukar dai kuna so auren 'ya'yanku yayi albarka.
Sannan ku guji zurfafawa ko
tsanantawa game da kayan lefe tunda babu shi acikin tsarin aure na musulunci.
Al'adah ce ta kawoshi. Don haka arika sassautawa ana yin nasiha ga ɓangaren gidan maza cewar
kada su matsa wa kansu, su kawo abinda ya sawwaka kawai. Kuma adena la'akari da
cewar ai an kawo wa wance kaza-da-kaza, don me mu ba za'a kawo wa tamu 'diyar
ba!!!
Muyi koyi da Manzon Allah
(Sallallahu alaihi Wasallam) tunda auren nan dai sunnarsa ne. Mu guji aikata
abinda zai kwashe albarkar auren.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.