Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Rufe Musulmi Hade Da Arna!

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Dr muna son karin hasken shari’ar Musulunci akan yadda sojoji ke bikin karrama matansu da kuma yadda suke rufe Musulmi da wadanda ba musulmi ba a makabarta ɗaya.?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, Malaman musulunci suna cewa: Ba’a rufe musulmai da kafirai a makabarta ɗaya kuma hakan shi ne aikin magabata tun zamanin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam har zuwa yau daga cikin dalilai akan haka shi ne manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya wuce makabartar kafirai sai ya ce wadannan alkairi ya rigaye su, da kuma ya wuce makabartar musulmai sai ya ce wadannan sharri ya rigaye su kamar yadda Nisa’i ya rawaito, wannan sai ya nuna banbanci tsakanin makabartun biyu.

Idan aka rufe musulmi a makabartar kafirai in an yi musu azaba za ta same shi, saboda aya ta: 46 a suratu Gafir ta nuna ana yi musu azaba a kabarinsu

النَّارُ يُعْرَضُونَ عَلَيْهَا غُدُوًّا وَعَشِيًّا ۖ وَيَوْمَ تَقُومُ السَّاعَةُ أَدْخِلُوا آلَ فِرْعَوْنَ أَشَدَّ الْعَذَابِ

Wutã, anã gitta su a kanta, sãfe da maraice, kuma a rãnar da Sa'a take tsayuwa, anã cwa, ''Ku shigar da mutãnen Fir'auna a mafi tsananin azãba.'' (Suratul Gafir Aya ta 46)

Yin bukukuwa yayin bunne musulmi ya saɓawa ka’idojin sharia sanannu, don haka ya kamata musulmi su jarraba amsar gawarsu mutukar hakan zai yiwu.

Allah ne mafi sani.

Don neman Karin bayani duba Al-mugni na Ibnu-khudaamah 2/563

DR JAMILU ZAREWA

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments