Ticker

6/recent/ticker-posts

Mafi Karancin Sadaki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullah. Tambayoyi akan Mafi karancin sadaki sun Yi yawa, musamman yadda naira ta karye, rayuwa ta shiga tasku, hidimomi suka hau kan mutane. Malam ko akwai wani nassi ingantacce wanda ya iyakance mafi karancin sadaki ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. Babu wani nassi bayananne yankanke da ya yi bayanin mafi karancin sadaki, sai dai kiyasi da tsantsar ijtihadi .

A mazhabar Malikiyya mafi karancin sadaki shi ne 1/4 na dinare, kwatankwacin sama da naira (100,000) a halin yanzu, sai dai sun kafa hujja ne da kiyasi, inda suka ce ana yanke hannun barawo idan ya saci Ɗaya cikin huɗu na dinare, saboda haka aka batar masa da gaba, aka yanke ta, saboda 1/4 na dinare, to shi ma Wanda ya auri mace zai batar mata da wata gaba a jikinta (budurci), wannan ya sa suka Yi tarayya a hukunci، don haka, ba ya halatta a biya kasa da 1/4 na dinare, kamar yadda Ibnu Abdulbarr ya ambata a littafinsa Attamhid 2/186.

A wajan mafi yawancin malamai ya halatta duk wani abu mai kima a idon mutane ya zama sadaki ko da kuwa naira (5) ce, sun kafa hujja da hadisin da Bukhari da Muslim suka rawaito, inda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya aurawa wani sahabinsa wata mace, Amma sadakinta shi ne wasu daga cikin surorin Alkur'ani, ba a ba ta ko sisi ba.

Mazhabar Malikiyya a wannan matsalar tana da karfi, saboda hakan zai karawa aure daraja da martaba a idon miji, sai dai wanda ya ba da kasa da haka a matsayin sadaki, auransa ya inganta saboda rashin samun nassi bayananne akan mas'alar, sai ijtihadi, wannan yasa a Saudiyya har akan riyal Ɗaya ana iya halattawa miji mace.

Wanda ya bada naira (1,000) a matsayin sadaki, auransa ya dauru, Amma in ya bayar da kuɗi masu yawa zai samu lada mai yawa, wannan yasa Umar (RA) ya fasa yanke mafi yawancin sadaki saboda ayar da ta zo suratun Nisa'i.

Don neman karin bayani a duba Bidatul Mujtahid wa nihayatul Muktasid

Allah Ne mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments