Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Manta Ba Ta Yi Wankan Tsarki Ba (Hukuncin Salla Da Maniyyi a Jikin Tufafi)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. A daren azumin farko ta yi janaba amma ta manta ba ta yi wanka ba, sai a ranar azumi na biyu ta tuna, to ina matsayin azuminta da sallarsa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Samuwar janaba a cikin dare ba ta hana yin azumi. Domin A’ishah da Ummu-Salamah (Radiyal Laahu Anhumaa) sun riwaito cewa

أَنَّ رَسُولَ اللهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ -، كَانَ يُدْرِكُهُ الفَجْرُ وَهُوَ جُنُبٌ مِنْ أَهْلِهِ، ثُمَّ يَغْتَسِلُ وَ يَصُومُ

Haƙiƙa! Alfijir yakan riski Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi wa Alihi wa Sallam) a halin yana da janaba daga iyalinsa, sai kuma ya yi wanka ya cigaba da azumi. (Sahih Al-Bukhaariy: 1926, Sahih Muslim: 1109).

Wannan ya nuna samuwar janaba a cikin dare ba ya hana yin azumi, ko da kuwa ba a yi wanka ba sai a bayan ketowar alfijir.

Haka kuma dangane da mafarki a cikin yinin azumi malamai sun ce

الاحْتِلَامُ بِالنَّهَارِ لَا يُفْسِدُ الصَّومَ

Fitar maniyyi a cikin barci da rana ba ya ɓata azumi. (Bidaayatul Mujtahid: 1/546).

Amma maganar sallah ce akwai matsala. Tun da yake tsarkin hadasi sharaɗi ne ga sallah saboda maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

« لاَ تُقْبَلُ صَلاَةٌ بِغَيْرِ طُهُورٍ ».

Allaah ba ya karɓar sallah ba tare da tsarki ba. (Sahih Muslim: 557).

Don haka ya zama dole in ji malamai, ga wanda ya samu kansa a cikin irin wannan mantuwar ya ramo dukkan sallolin da ya yi daga lokacin da janabar ta same shi har zuwa lokacin da ya tuna.

A nan malamai suna kawo athar na Umar Bn Al-Khattaab da Uthmaan Bn Affaan (Radiyal Laahu Anhumaa) da irin wannan ta shafe su, wato sun yi wa mutane limanci alhalin suna da janaba. Kuma da suka tuna a bayan haka sai suka sake sallar. Ba su hori sauran jama’a da maimitwa ba. (Al-Baihaqiy ya fitar da su a cikin Sunan Al-Kubraa: 3877-3878).

Allaah ya ƙara mana fahimta.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐍𝐀 𝐆𝐀 𝐖𝐀𝐍𝐃𝐎𝐍𝐀 𝐀 𝐉𝐈𝐊𝐄 𝐃𝐀 𝐌𝐀𝐍𝐈𝐘𝐘𝐈 𝐁𝐀𝐘𝐀𝐍 𝐍𝐀 𝐊𝐀𝐌𝐌𝐀𝐋𝐀 𝐒𝐀𝐋𝐋𝐀𝐑 𝐋𝐀'𝐀𝐒𝐀𝐑

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam na tashi da safe sai nayi Sallar Asuba da Azahar da kuma La'asar, bayan naje wanka da yamma naga wandona da alamun maniyyi. Shin ya ingancin sallolina na baya? Nagode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. Mutukar ka tabbatar a baccin Asuba maniyyin ya fito, to ya wajaba ka sake Asuba da Azahar da La'asar ɗin. In har ka yi wani baccin bayan Azahar to za ka danganta janabar ne zuwa ga baccin ƙarshe da kayi, ta yadda sallar da kayi bayan baccin ƙarshe ita za ka sake, kamar yadda Imamu Malik ya rawaito a Muwadda daga Sayyady Umar.

Allah ne mafi sani.

𝑨𝒎𝒔𝒂 𝒅𝒂𝒈𝒂 𝑫𝒓. 𝑱𝒂𝒎𝒊𝒍𝒖 𝒀𝒖𝒔𝒖𝒇 𝒁𝒂𝒓𝒆𝒘𝒂

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐁𝐔𝐒𝐀𝐒𝐇𝐒𝐇𝐄𝐍 𝐌𝐀𝐍𝐈𝐘𝐘𝐈 𝐀 𝐉𝐈𝐊𝐈𝐍 𝐑𝐈𝐆𝐀

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam akwai wata riga ta da na jima ban sanya ba, yanzu na ɗauko sai na ga maniyyi busashshe a jiki, yaya zan yi da shi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. Abinda yake kanka shine; ka kankare shi, kamar yadda Nana A'isha take yi da maniyyin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) idan ya bushe a jikin rigar shi.

Allah ne mafi sani.

𝑨𝒎𝒔𝒂 𝒅𝒂𝒈𝒂 𝑫𝒓. 𝑱𝒂𝒎𝒊𝒍𝒖 𝒀𝒖𝒔𝒖𝒇 𝒁𝒂𝒓𝒆𝒘𝒂

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐍𝐀 𝐘𝐈 𝐖𝐀𝐍𝐊𝐀𝐍 𝐉𝐀𝐍𝐀𝐁𝐀 𝐒𝐀𝐈 𝐌𝐀𝐍𝐈𝐘𝐘𝐈 𝐘𝐀 𝐒𝐀𝐊𝐄 𝐙𝐔𝐁𝐎 𝐌𝐈𝐍

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Tambaya ta ita ce: Idan mace ta sadu da mijinta tayi wanka bayan sun gama, tana zaune sai ta ji maniyyi ya zubo mata, shin za ta ƙara yin wani wankan ko kuma wanda tayi ya isa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. To idan sabuwar sha'awace tazo mata ta zubar da maniyyi, ya wajaba ta sake wanka, amma idan saboda saduwar da suka yi ne a baya, za ta wanke wurin ne kawai ta sake alwala, amma babu bukatar sake wanka, wanda tayi na farko ya isa.

Duba: Bidayatu Almujtahid 1/48 da Insaf 1/232.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments