𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Wanda ya kwanta barci da janaba bai tashi ba har zuwa lokacin sahur, har aka yi sallar Asubah, gari ya waye. Yaya zai yi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah Wa Barakaatuh.
Al-Imaam Al-Bukhaariy (1926) da
Al-Imaam Muslim (2649) sun riwaito daga A’ishah da Ummu-Salamah (Radiyal Laahu
Anhumaa) cewa
أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ
- كَانَ يُدْرِكُهُ الْفَجْرُ وَهُوَ جُنُبٌ مِنْ أَهْلِهِ ، ثُمَّ يَغْتَسِلُ وَيَصُومُ
Haƙiƙa! Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam) alfijir yakan riske shi a halin yana da janaba daga iyalinsa,
sannan sai ya yi wanka kuma ya yi azumi.
Wannan hadisi ya nuna
1. Ya halatta musulmi ya kwanta
ya yi barci alhalin yana da janaba ko da daga iyalinsa ne ya same ta, ba ma wai
ta hanyar mafarki ba.
2. Abin da aka fi so ga mai
janaba shi ne ya fara kawar da ita ta hanyar yin wanka kafin yin barci, in kuwa
hakan bai samu ba to sai ya yi alwala, kamar yadda wasu riwayoyin suka nuna.
3. Ko da alfijir ya fito alhali
mutum yana da janaba bai riga ya yi wanka ba, wannan ba ya hana shi cigaba da
yin azuminsa na wannan yinin.
4. Bai halatta mai janaba ya bari
har lokacin sallah ya shiga alhali bai yi wanka ba, sai fa in da wata larura ce
da Shari’a ta yarda, kamar barci ko mantuwa da sauransu.
5. Ba daidai ba ne mai son yin
azumi ya tashi ya yi sahur amma kuma ya koma ya cigaba da barci ba tare da ya
yi shirin sallar Asubah ba, har sai da gari ya waye.
5. Duk wanda ya bar lokacin wata
sallar Farilla ya fita da gangar ba da wani uzuri karɓaɓɓe
a Shari’a ba, to yana da zunubi mai girman gaske, wanda wasu malaman ke ganin
ko rama sallar ma bai isa ya kankare shi ko ya kawar da shi ba!
6. Wajibi ne a kan duk wanda ya
aikata wannan ya yawaita tuba kuma ya yawaita neman Allaah (Subhaanahu Wa
Ta’aala) ya gafarta masa, ya yafe masa, kuma ya yawaita ayyukan nafila don
neman tsira a Lahira.
Allaah ya shiryar da mu gaba-ɗaya.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Turo tambayar ta WhatsApp number,
banda kira ko tambayar gaggawa. 08164363661
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.