Ticker

6/recent/ticker-posts

Lokacin Yin Sallar Dare

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Ina son yin sallar dare, amma ba na iya farkawa ƙarfe biyu (2: 00am), to ko zan iya yi ƙarfe sha-ɗaya (11: 00pm) ko sha-biyu (12: 00am) ko kuma ƙarfe ɗaya (1: 00am)?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Lokacin sallar dare (Qiyaamul Laili) yana farawa ne daga bayan gama sallar isha’i har zuwa fitowar alfijir. Don haka, ya halatta mutum ya yi wannan sallar a tsakanin waɗannan lokutan guda biyu, ko da a bayan gama sallar isha’i ne nan-take. Babu wata takurawa ko damuwa a kan haka, musamman ga wanda ba ya iya farka wa a ƙarshen daren.

Amma dai an fi son a kai sallar ce zuwa ƙarshen dare, kafin fitowar alfijir ga wanda ya samu iko, saboda fa’idoji kamar haka

1. A lokacin an fi samun jin daɗin ganawa da Ubangiji, domin bayan farkawa daga barci jiki ya samu hutawa, kuma zuciya ta samu ƙarin natsuwa.

2. A lokacin yanayin gari yana da daɗi, akwai sanyi da ƙarancin zafi, kuma akwai iska mai daɗi, don haka akwai natsuwar zuciya da jiki a wurin ganawa da Mahaliccinmu (Tabaaraka Wa Ta’aala).

3. A lokacin mala’iku suna kusa da saukowa domin halartan sallar Asubah a cikin masallatai a bayan ketowar alfijir, don haka akwai sa-ran amsar addu’o’in masu yin sallah a lokacin.

4. A lokacin ne Allaah Ta’aala yake saukowa zuwa saman duniya yana cewa: Wa zai yi addu’a gare ni in amsa masa? Kuma wa zai roƙe ni in ba shi buƙatarsa? Kuma wa zai nemi gafarata in gafarta masa?

(Al-Bukhaariy: 7494; Muslim: 758)

Allaah ya datar da mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Turo tambayarka ta WhatsApp number, banda kira ko tambayar gaggawa. 08164363661

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments