Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Biyawa Kanta Buqata Ba Tare Da Namiji Ba A Lokacin Ramadan

TAMBAYA (82)

Aslm ina wuni malan ya gida matar aurece a aximi tabiyawa kanta bukata batareda namijiba shin xata biya aximinne ko Wanda Tasha kawai xatayi sannan xata biya aximin a wannan shekaran ko duk lokaçinda tatashi

Yanxu Ramadan yawuce ga wani Ramadan yaxo xata Rama bayan Ramadan din Nan kenan tahada da Wanda Tasha na wannan Ramadan din

AMSA

Alhamdulillah

Na'am

Zata rama wancan ne bayan Ramadan dinnan ya wuce

Amman kam ta fiya sakaci dayawa, ace har azumi ya kewayo Amma batasan hukuncin wancan azumin da ta karya ba silar masturbating din

Yin wasa da al'aura (masturbation) haramun ne kamar yanda Malamai mafi rinjaye suka fada, kana azumi ne ko kuma baka azumi

Idan kana azumi kuma kayi wasa da gabanka har maniyyi ya fito to azumin nan ya karye. Idan maniyyi bai fito, azumin ka yananan

A cikin Al-Mughni, Ibn Qudaamah yace: "Duk wanda yake wasa da al'aurarsa to zunubi yake aikatawa. Saidai azumin mutum yananan ko da ya aikata Istimna'i amman idan ya fitar da maniyyi, azuminsa ya karye"

A cikin dai Al-Mughni din ya ci gaba da cewa: ”Duk wanda ya fara azumin nafila kuma ya karyashi to ba a binsa ramuwa duk da cewar ramawar shi yafi (Mustahabbi ne). Wanda duk ya fara azumin nafila to ya kammala shi. Duk wanda ya karyashi to ba sai ya rama ba tunda daman ba na farillah bane ba

Abdullahi Ibn Umar da kuma Ibn Abbas (Radiyallahu anhum) sun taba daukan azumin nafila wata rana kuma wani dalili yasa suka karya shi. Ibn Umar yace: "Babu laifi saidai idan mutum yana azumin da ake binsa ne ko kuma azumin rantsuwa"

Al-Mughni: " An-Nakha'i, Abu Haneefah, Imam Maleek since: "Duk wanda ya fara azumi to ya cika shi. Kada ya karya shi har saidai idan akwai wani qwaqqwaran daleel (dalili) wanda zaisa ya rama daga baya"

A karshe kuma a shawarce ta dage da yawaita Istighfari, tayi taubatun Nasuha kuma kada ta kara kusantar duk wani abu da ka iya zama silar karyewar azuminnata

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments