Ticker

6/recent/ticker-posts

Allah Ya Kara Wa Annabi ﷺ Daraja

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Nakan ji mutane suna faɗin wannan kalmar: ‘Allaah ya ƙara wa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) daraja. Shin ko wannan daidai ne?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Idan ana nufin sanin hukuncin yi masa addu’a da hakan ne kawai, wato a roƙa masa ƙarin daraja daga Allaah da waɗannan kalmomin, wannan a fahimtata ba laifi ba ne, in sha Allah. Domin a cikin Alqur’ani Allaah Ta’aala ya ce

إِنَّ اللَّهَ وَمَلَائِكَتَهُ يُصَلُّونَ عَلَى النَّبِيِّ يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا صَلُّوا عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا تَسْلِيمًا

Haƙiƙa Allaah da Malaikunsa suna yi wa Annabi salati. Ya ku waɗanda suka yi imani, ku yi masa salati kuma ku yi sallama cikakkiyar sallama. (Surah Al-Ahzaab: 56).

Al-Haafiz Ibn Hajr Al-Asqalaaniy ya ambato fassarar Salati, wadda ya ce ita ce duk ta fi, daga Abul-Aliyah cewa:

مَعْنَى صَلَاةِ اللهِ عَلَى نَبِيِّهِ: ثَنَاؤُهُ عَلَيْهِ وَتَعْظِيمُهُ، وَصَلَاةُ الْمَلَائِكَةِ وَغَيْرِهِمْ عَليْهِ: طَلَبُ ذَلِكَ لَهُ مِنَ اللهِ تَعَالَى، وَالْمُرَادُ طَلَبُ الزِّيَادَةِ لَا طَلَبُ أَصْلِ الصَّلَاةِ

Ma’anar salatin Allaah ga Annabi shi ne yabonsa a gare shi da kuma girmama shi. Salatin Mala’iku da mutane kuwa shi ne: Neman hakan gare shi daga Allaah Ta’aala. Wato neman Allaah ya ƙara masa hakan, ba neman asalin salatin ba. (Fat-hul Baariy: 11/156).

Don haka, neman Allaah ya ƙara wa Annabi Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ƙarin girma da ɗaukakar daraja ta wannan fuskar ba laifi ba ne.

Amma idan ana nufin mayar da wannan wata kalmar maimaitawa a kowane lokacin murna ko farin ciki da makamantan hakan, wannan kam matsala ne. Domin ban san aikata hakan a cikin magabatan wannan al’ummar ba, waɗanda kuwa su suka fi na-bayansu cikan imani da taqawa da ƙaunar Allaah da Manzonsa, kuma su suka fi kowa gudun saɓa wa Allaah da Manzonsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Shiyasa bin hanyarsu a cikin komai ya zama shi ne kaɗai hanyar tsira, kamar yadda ya ke a wurin Ahlus-Sunnah.

Idan kuwa ana ƙoƙarin mayar da wannan kalmar ta zama a duk lokacin da aka kira sunansa ne, to wannan kuma kuskure ne a fili. Domin ya saɓa wa abin da shi kansa Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa

« الْبَخِيلُ الَّذِى مَنْ ذُكِرْتُ عِنْدَهُ فَلَمْ يُصَلِّ عَلَىَّ ».

Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa amma bai yi mini salati ba. (Sahih At-Tirmiziy: 3546).

Wannan ya nuna abin da ya ke daidai shi ne a yawaita yi masa salati a duk lokacin da aka ambaci sunansa a wurin musulmi, da irin lafazin salatin da ya koya wa sahabbansa a cikin rayuwarsa kafin rasuwarsa, ba waccan addu’ar ba.

Wannan shi ne abin da na fahimta daga wannan mas’alar.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁��𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments