Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halatta Ga Mace Mai Haila Ta Shiga Masallaci?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘��

Shin ya halatta ga mace mai haila ta shiga masallaci? Don Allah malam ka amsa mana tambayar nan domin yanzu haka musu mukeyi da wasu mata. Sunce wai ba'a hana ba. Wai inji su Sallah ce kawai aka hana suyi. Amma ba'a hana su shiga masallaci su zauna ba. Malam yaya abun yake ne?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Dukkan Maluman mazhabobin nan huɗu sunyi ittifaki akan rashin halaccin shigar mace mai haila cikin masallaci.

Duk sunce bai halatta ba. Kuma hujjarsu anan ita ce hadisin da bukhary da muslim suka ruwaito daga Ummu Atiyyah (rta). Tana cewa

"Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya umurcemu mu fito da 'yan mata, da matayen da suke tsari (domin suzo masallacin Eidi.) Amma Yace masu haila su nisanci masallacin musulmai"

(Aduba Sahihul Bukhary hadisi na 974, sahihu MusLim hadisi na 890)

Malamai suka ce Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya umurcesu suyi nesa da masallacin Eidi ne saboda matsayinsa kamar masallacin jumu'a ne da sauran masallatai.

Acikin FATAWAL LAjNATUD DA'IMAH juzu'I na 6 shafi na 272, an tambayi majalisar malaman sa'udiyya. Shin mace mai haila zata iya shiga masallaci domin ta zauna ta saurari Khutbah ko wa'azi ko karatun Alkur'ani?

Sai suka ce A'a bai halatta ba gareta ko ga mai jinin haihuwa su shiga masallaci su zauna. Sai dai idan larura tasa, zasu iya shiga su wuce ta cikin masallacin. Amma idan batta tsoron kada jinin nata ya zuba ya ɓata shimfidar masallacin yayin wucewar tata. Kamar yadda ayah ta 43 acikin suratun Nisa'I tayi bayani

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَقْرَبُوا الصَّلَاةَ وَأَنْتُمْ سُكَارَىٰ حَتَّىٰ تَعْلَمُوا مَا تَقُولُونَ وَلَا جُنُبًا إِلَّا عَابِرِي سَبِيلٍ حَتَّىٰ تَغْتَسِلُوا ۚ وَإِنْ كُنْتُمْ مَرْضَىٰ أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ أَوْ جَاءَ أَحَدٌ مِنْكُمْ مِنَ الْغَائِطِ أَوْ لَامَسْتُمُ النِّسَاءَ فَلَمْ تَجِدُوا مَاءً فَتَيَمَّمُوا صَعِيدًا طَيِّبًا فَامْسَحُوا بِوُجُوهِكُمْ وَأَيْدِيكُمْ ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَفُوًّا غَفُورًا

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kusanci sallah alhãli kuwa kuna mãsu mãye, sai kun san abin da kuke faɗa kuma haka idan kuna mãsu janaba, fãce mai ƙetare hanya, har ku yi wanka. Kuma idan kun kasance majinyata, ko kuwa a kan tafiya ko kuwa wani daga cikinku, idan ya zo daga gayaɗi, kõ kuwa kun shãfi mãtã ba ku sãmi ruwa ba, to ku nufi, fuskar ƙasa mai kyau, ku yi shãfa ga fuskokinku da hannuwanku. Lalle ne Allah Yã kasance Mai yãfewa Mai gãfara. (Suratun Nisá'i Aya ta 43)

An tambayi Shaykh Ibnu uthaymeen game da haka shima yace Bai halatta ba. Domin hukuncin mai haila kamar na mai janaba ne. Kuma ya kawo hujjoji akan rashin halaccin hakan.

(Aduba littafinsa mai suna Fatawat tahaarah shafi na 273).

Idan kana son kaga qarin bayani da kuma sauran maganganun malamai akan haka, kaje ka duba wadannan litattafan

1. ALMABSOOT juzu'I na 3 shafi na 153.

2. HASHIYATUD DASOOQEE juzu'I na daya shafi na 173.

3. ALMAJMOO'U na Nawawy, juzu'I na 2 shafi na 388.

4. ALMUGHNEE na ibnu qudamah, juzu'I na 1 shafi na 195.

Ina fatan mutane zasu rika zurfafa bincike akan manyan mas'aloli irin waɗannan. Adena yarda da maganganu na sonrai marasa hujjoji.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DIcJIQrWyLP0oBOMSnDi5P

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments