Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Auri Dan Duba - Yanzu Kuma Tana Son Rabuwa Dashi

TAMBAYA (77)

Assalamu alaikum malam barka da warhaka da fatan kana cikin koshin lfy yayatace ta auri malamin duba kafin auren nasu antambayi wani malami sai yabasu tarihin fir.auna da matassa asiya sai suka gamsu bayan anyi Auren kuma sai taji wani malami ya ce wallahi duk jikin da yaginu da haramu wutane zaici sai hankalinta ya tashi sosai Dan allah malam ataimaka a amsamin wannan tambaya nagode

AMSA

Alhamdulillah

Allah (Subhanahu wata'ala) ya ce;

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُلُوا مِن طَيِّبَاتِ مَا رَزَقْنَاكُمْ وَاشْكُرُوا لِلَّهِ إِن كُنتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ )

البقرة (172) Al-Baqara

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ci ku sha daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku. Kuma ku gõde wa Allah, idan kun kasance Shi kuke bauta wa.

( يَا أَيُّهَا الرُّسُلُ كُلُوا مِنَ الطَّيِّبَاتِ وَاعْمَلُوا صَالِحًا ۖ إِنِّي بِمَا تَعْمَلُونَ عَلِيمٌ )

المؤمنون (51) Al-Muminoon

Yã ku Manzanni! Ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩga abin da kuke aikatãwa, Masani ne.

Wadannan ayoyin gaba daya suna mana nuni ne akan cin halak

Haka kuma an karbo hadisi daga Sayyadina Abubakar (Radiyallahu anhu) ya ce: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce; "Duk jikin da ya ginu da haram bazai shiga Aljannah ba"

(Sunan Baihaqi)

An karbo hadisi daga Ka'b Bin Ujrah (Radiyallahu anhu) ya ce: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce; "Duk jikin da ya ginu da haram bazai shiga Aljannah ba"

(Sunan Tirmizi)

An karbo daga Jabir Bin Abdullah (Radiyallahu anhu) ya ce: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce; "Duk naman da ya ginu da haram ba zai shiga Aljannah ba, wutar jahannamah ita tafi cancanta dashi"

(Musnad Ahmad, Sunan Darimi da kuma Sunan Baihaqi)

A shawarce idan har abinda kika fada ya tabbata to bai kamata ta ci gaba da zama da wannan dan duban ba, sannan hadisi ya tabbata daga Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) cewar duk wanda ya je ya gasgata maganar dan duba to ya kafircewa abinda aka saukarwa Muhammad

Shi kuma wancan malamin wanda ya basu tarihin fir'auna da asiya, ya jahilci qissar. Kenan yana nufin idan mijin yayar taki shine fir'auna ita kuma yayar taki itace asiya ?

A ina ya samo wannan fahimtar ?

Indai ba so suke su halaka ba, ta gaggauta sanar da waliyyanta halin da ake ciki, amman ni a fahimta ta yayar taki ta bi son zuciyar ta ne ta aure shi, zata iya yiwuwa ya sakar musu kudi ne ita kuma ta rudu da haka la'akari da halin da ake ciki na tsadar rayuwa, shawara ta anan shine su je wajen alqali ita da waliyyanta su raba su indai har mijin na ta bazai tuba ya daina harkar duba dinnan ba

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments