Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Aske Sashe Na Gashin Kai A Bar Wata Sashe

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamun alaikum Malam Menene Hukuncin Aske Sashe Na Gashin Kai A Bar Wata Sashe A Musulunci?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahamtullahi Wabarkatuh

Lallai yana daga abubuwan da aka jarabci da yawa daga cikin mutane a yau musamman matasa, canza wa kawunansu kamanni ta hanyar aske sashe na gashin Kansu da sunan ado musamman a bukukuwan sallah, Wanda galibinsu kwafoshi sukeyi daga wurin wasu mashahuran arna da kafurai, waɗanda mafi yawansu sun jahilci hukuncin hakan a Musulunci, wanda da sun sani da sun nisanceshi.

An karbo hadisi daga Ibn Umar Allah ya qara masa yarda ya ce: "lallai Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yayi hani akan ALQAZA'U. Ubaidullah ya ce wa Nafi'u: menene kuma ALQAZA'U? Sai ya ce: shine a aske sashe na gashin kan yaro abar sashe." Wannan hadisi Bukhari da Muslim suka rawaitoshi

A wani hadisin na Ibn Umar har wa yau ya ce: lallai Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yaga wani yaro an aske sashe na gashin kansa aka bar sashe, Sai ya hanesu akan hakan, ya ce: "Ku askeshi gaba ɗaya ko ku barshi gaba ɗaya".

Abu Dawuda da Ahmad suka rawaitoshi.

Malamai sunyi saɓani kan hukuncin irin wannan aski: Wasu sukace MAKARUHI ne, kamar mazhabar SHAFI'IYYAH da HANABILAH. Kamar yadda Imam Annawawy ya tabbatar da hakan acikin littafinsa ALMAJMU' 1/347 Kuma ya naqalto ijma'insu akan haka.

Wasu kuma sukace HARAMUN ne, saboda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yayi hani akan haka, sannan ya bada umurnin a askeshi gaba ɗaya ko a barshi gaba ɗaya a hadisai guda biyu da suka gabata.

Sukace: domin kalmar hani asali tana hukunta haramci ne, kamar yadda Kalmar umurni ke bada hukuncin wajibci.

Saboda haka sukace hadisan guda biyu suna nuni ne akan haramcin aske sashen kai da barin sashe.

To idan kuma ya kasance mai yin irin wannan askin ya kwafoshi daga wurin kafurai ko fajirai ko kuma wasu waɗanda shari'ah tayi hanin ayi koyi dasu, to wannan kai tsaye haramun ne har a wurin malaman da suke ganin Makaruhi ne, domin illar kamanceceniya da kafurai haramci ke nunawa,

Saboda hadisin Ibn Umar Allah ya qara masa yarda ya ce: lallai Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya ce: "Duk Wanda yayi kamanceceniya da wasu mutane to yana tare dasu".

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments