Shin Mai Haila Za Ta Iya Yin Zikiri?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum. girma da ɗaukaka su tabbata ga shugabanmu annabi Muhammadu (Sallallahu alaihi Wasallam) da ahlin gidansa da sahabbansa tsarkaka. Malam alkairin Allah ya tabbata agareka da sauran ɗaukakin al'umar musulmi baki ɗaya. Tambaya itace

    1. Nasan mutum me janaba ze iya zikiri, tasbihi da salati. Malam shin mace me haila itama zata iya aikata hakan?

    2. mutun ne ke zargin matarsa da yawan fita (unguwa) har ta kai ga ya saketa, in yana da bukatar mayar da ita ze iya?

    3. ina bukatar malam da yaja hankalin yan mata akan Half naked dress. wlh malam mu dake akasuwa muke ganin irin hatsabibiyar shigar dasuke abun kyama da kunya ne ga 'ya'yan musulmi.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

     Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.

    1. Ai hukuncin haila da janaba yakan zama iri guda acikin mafiya yawan mas'aloli.

    Bisa mazhabin Limamin gidan Hijira (Wato Imamu Malik) Ya halatta mace mai haila tayi kowanne irin zikiri. harda tilawar Alqur'ani (amma ba tare da ta taɓa Mus'hafin Alqur'anin ba).

    2. Mutumin da yake zargin cewa matarsa tana fita waje, har wannan zargin ya kai ga rabuwar aurensu, yana da damar ya sake dawo da ita amatsayin matarsa in dai sakin da yayi mata bai kai uku ba.

    Amma wasu Malaman sunce in dai zargin Zina yake yi mata, to babu damar ya sake mayar da ita matarsa har sai ya tuba daga wannan zargin da yake yi mata.

    Saboda shi Musulunci ba ya son zaman cutuwa. mutukar yana ci gaba da zarginta da zina, zai yiwu watarana idan ta haihu yace wannan yaron ba nasa bane. kaga kenan sai sunje sunyi Li'aani.

    3. Matayen da suke yin mummunan dressing, hakika Allah da Manzonsa ya tsine musu. Kuma Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) yace ba zasu shiga aljannah ba. kuma koda Qamshinta ma ba zasu ji ba.

    Kuma wannan alama ce da take nuna cewa sun riga sun amincewa da fushin Allah, sun yarda cewa su ribatattun Shaiɗan ne. Shi yasa ba zaka ga wani mutumin kirki yana kulasu ba. Sai dai Qazamai masu Qazantar tunani irin nasu.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.