Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Yin Gyatsa Tana Karya Azumi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaykum. malam ya ibada ? don Allah malam ka taimaka ka amsamin tambayoyina ina cikin rudu; malam shekaran jiya ina aikin abinci sai itace da nake amfani da su sai naji daya kamar yana wani kanshi wutar da nayi sai na shinshina itacen aiko sai hayaki ya shige min cikin hanci don Allah ya ya matsayin azumina yake ? sai kuma bayan nayi sahur sai inta gyatsa wani lokacin har cikin makoshina yaya matsayin azumi na yake ? don Allah ataemaka a amsamin albarkacin wannan watan.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullah.

1. Mace mai girki, hayakin itace ko Qamshin abinci ko tururin abinci duk basu karya mata azumi. Koda da gangan kika sheqi abun don neman sanin ko girkinki ya dahu.

2. Gyatsa bata karya azumi sai dai idan sauran abinci ya biyo ta makogoron mutum ko kuma ta hancinsa ta sanadiyyar gyatsar, sannan kuma ya sake hadiyeshi da gangan.

Amai (kumallo) shima ba ya karya azumi sai dai idan mutum ya janyo yin aman ne da gangan, ko kuma mutum ya sake hadiye sauran aman dake cikin bakinsa, to azuminsa ya karye. Zai rama guda ɗaya.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments