Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Dandana Abinci Ga Mai Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mutum ne yake azumi sai ya ɗanɗana girki, shi ne kuma yake waswasin ko ya haɗiye abin ko bai haɗiye ba. Yaya matsayin azuminsa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Da farko dai ya halatta mutum ya ɗanɗana wani abinci idan buƙatar hakan ta taso masa, kamar mai shirya abincin ko sayensa don ya gane yanayinsa. Abdullaah Bn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce:

لاَ بَأْسَ أَنْ يَذُوقَ الْخَلَّ ، أَوِ الشَّيْءَ مَا لَمْ يَدْخُلْ حَلْقَهُ وَهُوَ صَائِمٌ.

Babu laifi idan mutum ya ɗanɗana khal ko wani abin da yake son sayensa, matuƙar dai bai shiga maƙoshinsa ba, alhalin yana azumi. (Ibn Abi-Shaibah: 9369, kuma Albaaniy ya hassana shi a cikin Al-Irwaa: 4/86).

To, idan mutum ya aikata irin wannan abin da aka halatta masa a shari’a, kamar ya shaƙa ruwa ko ya kurkure baki a wurin alwala, ko ya tattauna wa ƙaramin yaro abinci, ko kuma ya ɗanɗana abincin a kan harshensa, sai kuma abincin ya zarce ya shige cikin maƙogwaronsa a bisa kuskure ba da gangar ko da son ransa ba, a nan malamai sun sha bamban.

Amma maganar da ta fi daidai in Shã Allahu ita ce: Azuminsa yana nan daram, bai ɓaci ba saboda dalilai irin waɗannan

Allaah Ta’aala ya ce

وَلَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ فِيمَا أَخْطَأْتُمْ بِهِ وَلَكِنْ مَا تَعَمَّدَتْ قُلُوبُكُمْ

Kuma babu wani laifi a kanku a cikin abin da kuka yi kuskure a kansa, sai dai kawai abin da zuciyarku ta ganganta. (Surah Al-Ahzaab: 5).

Sannan kuma Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« إِنَّ اللَّهَ تَجَاوَزَ عَنْ أُمَّتِى الْخَطَأَ وَالنِّسْيَانَ وَمَا اسْتُكْرِهُوا عَلَيْهِ ».

Haƙiƙa! Allaah ya yafe wa alummata kuskure da mantuwa da abin da aka tilastata a kansa. (Sahih Ibn Maajah: 1662).

Kuma da ma abu ne sannane daga Sunnar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

« مَنْ نَسِىَ وَهُوَ صَائِمٌ فَأَكَلَ أَوْ شَرِبَ فَلْيُتِمَّ صَوْمَهُ فَإِنَّمَا أَطْعَمَهُ اللَّهُ وَسَقَاهُ ».

Wanda ya manta a halin yana azumi sai ya ci ko ya sha, to ya kammala azuminsa domin Allaah ne kawai ya ciyar da shi kuma ya shayar da shi. (Sahih Al-Bukhaariy: 6669, Sahih Muslim: 2772).

Idan mun fahimci wannan, to ina kuma wanda a bayan ya ɗanɗana ne kuma yake shakkar cewa ko abincin ya shiga ko bai shiga maƙogwaronsa ba? Wannan shi ya fi cancantar a tabbatar da rashin ɓacin azuminsa, in Shã Allãh.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖��𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments