Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Karya Azumi Da Gangan

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam tambayata itace: menene hukuncin Wanda yasha Azumi da gangan? Kuma menene hukuncin samari da yan mata da suke biyawa kansu bukata alhali suna azumi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikum Salaam:- Karya Azumi da Gangan Haramun Ne Kuma Yana Daga Cikin Manya-Manyan Laifuka a Wajen Allahu Subhanahu Wata'ala. Don Haka Duk Wanda Ya Karya Azumin Na Rana Ɗaya tak ba tare da Wani Uzuri Mai Karfi Wanda Shari'ar Musulunci Ya Yarda Da shi ba, Kuma Ɓai Tuba ba, toh Babu Abin da Wannan Mutumin Zai Yi Ya isar Masa da Azumin Sa, Koda Kuwa Yayi Azumin Zamani Guda Gaba ɗayanta, toh bai Taɓa isar masa da Wannan Azumin guda 1 Tak da Ya Karya Shi da Gangan Nan.

Saboda Faɗin Annabi Muhammad Mai Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Agare Shi, (( Duk Wanda Ya Karya Azumi Rana ɗaya daga Cikin Ramadan, Ba a AKan Wani Rangwame da Allah Yayi Masa ba, toh Azumin Zamani gaba ɗaya ba Zai iya Rama Masa Wannan Azumin nasa guda Dayan Nan ba. Duba Cikin Dawud))

Mutum Yayi Asara Babba Wallahi, Azabar Allah Ya Tabbata ga Wanda Ya Karya Azuminsa da Gangan, Azaba mai Girma. An Karɓo Hadisi Daga Abu Umaimata Al-Bahili Allah Ya Kara Yarda Gare Shi, Yace Na Ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalam Yana Cewa, Ina Cikin Barci, Sai Wasu Mutane Ɓiyu 2 Suka Zo Min, Sannan Suka Tafi da Ni, Sai Kawai Na ga Wasu Mutane An Rataye Su ta Agarar Su, Muqamuqansu a Tsatsassage, Jini Yana ta Ƙwarara. Sai Ya Ce, Na Ce Shin Su Wanene Waɗannan? Sai Ya Ce, Waɗannan Waɗanda Suke Karya Azumin Su ne Tun Gabanin Lokacin Shan Ruwa Yayi)) Duba Cikin (Ibn Hibban)

Muna Kira Zuwa ga Matasa da Ƴan Mata Wallahi Ku ji Tsoron Allah Ku Sani Cewa Mutuwa zata Zo mu Ku a Lokacin da Ba ku Shirya mata Zuwa ba. Wallahi Kada Budurcin Ki, Balagar ki Kuruciyar ki Ya Kai ki ga Saɓawa Allah Wanda Za'a Miki Azaba Mai Raɗaɗi a Ranan Alkiyama Musamman na Qin yin Azumin Watan Ramadan.

Abin Mamaki ne wai Ana yin Azumi Ana Neman Gafaran Allah, Amma Wasu Ƴan Matan Biyawa Kansu Bukata Suke yi gurin Kallon Alfasha Tsiraicin Arna, har Sai ta Fitar da Maniyyi ko Maziyyi da Ranan Alhali Kuma Ana Azumi. Hakanan Maza Samari Wani Budurwa Yake Ɗaukowa Yana Zina da Ita da Rana a Cikin Watan Azumi Kuma Dukkan Su Musulmai ne Inna illahi Wa'inna illahin Rajee'um Subhanallah.

 Wanne Irin Masifa ce Wannan? Wanne Irin Bala'i Ce Wannan? Ke Kina Son Biyawa Kanki Bukata Menene Zai Hanaki Yin Aure Koda Babu Kayan Lefe da Sauran su? Kin Sa Buri a Ranki Samari Sun Ki Zuwa Ga Sha'awa na Tayar ki Kin ga Gara Bin Umurnin Allah da Manzon Allah Kin qi Yin Aure Yaya Ba Za ki Rika Saɓawa Allah ba? Daga Karshe Allah ya ɗauki Ranki ba ki Shiryawa Mutuwa me Za ki gayawa Ubangijin ki? Wallahi Ku Ji Tsoron Allah Ƴan Mata da Samari har da Matan Aure Masu Irin Waɗannan Ayyukan, Ba Zaku Taɓa Tsira a Gaban Allah ba a Ranan Alkiyama. Allah Ya Tsare ya Shirya.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments