Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halatta Mutum Ya Yi Raka'atanul Fajr Idan Bai Sami Jam'in Asuba Ba?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Ya Halatta Mutum Yayi rak'atayil fajr idan bai samu jam'in sallar asubah ba har gari yafara haske, zai fara yin sallar asubah ne ko kuma nafilar zai fara yi?   

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

Da farko dai wajibi ne akan kowanne musulmi ya kiyaye sallah akan lokacin ta. Allah maɗaukakin sarki Ya ce

إِنَّ الصَّلَاةَ كَانَتْ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ كِتَابًا مَّوْقُوتًا 

Lalle ne sallah ta kasance akan muminai farilla mai kayyadaddun lokuta. (Suratul Nisá'i Aya ta 103)

Lokacin sallar asuba shine daga fitowar alfijir na biyu har izuwa hudowar rana.

Baya halasta jinkirta sallah har lokacin ta ya fita. Saboda yin haka da gangan yana daga cikin manyan kaba'ira. Saɓanin wanda ya manta sallar ko kuma barci ya rinjaye shi ba da gangan ba, shi wannan abun yiwa uzuri ne.

Manzon Allah Yace

_"ﻣﻦ ﻧﺴﻲ ﺻﻼﺓ ﺃﻭ ﻧﺎﻡ ﻋﻨﻬﺎ ﻓﻠﻴﺼﻞ ﺇﺫﺍ ﺫﻛﺮﻫﺎ، ﻻ ﻛﻔﺎﺭﺓ ﻟﻬﺎ ﺇﻻ ﺫﻟﻚ" ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ.

Wanda ya manta sallah ko yayi barci akanta (barci a lokacinta) to ya sallaceta idan ya tina ta (sallar), kuma babu kaffara sai wannan (ramawar). Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.

Sallar asuba raka'a biyu ne, a gabanin su akwai raka'a biyu na nafilah ana kiransu "Sunnatul Fajr" ko "Sunnatus Subhi" ko "Ragiibatul Fajr" ko "Rak'atayil Fajr".

Idan mutum ya rasa jam'in asuba ya halatta mutum yayi rak'atayil fajr kafin yayi sallar asuba. Koda rana ta fito ne zai iya yin sallar rak'atayil fajr kafin yayi sallar asuba. Amma fa ba wanda ya rasa jam'i da gangan ba, saidai kamar wanda barci ya rinjayeshi har gari ya waye.

Kamar yadda yazo a Bukhari da Muslim da Sunan Abu Dawuda cewa: Haqiqa ya tabbata cewa barci ya rinjayi Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam da Sahabbansa a wata tafiya, basu farka ba har rana tafito sai suka sallaci rak'atayil fajr sannan suka sallaci asuba.

A wata ruwaya akace Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya umarci da a kira sallah sannan ya sallaci raatiibat (rak'atayil fajr), sannan ya umarci ayi iqaamah bayan haka sai ya sallaci farillah (sallar asuba).

Saboda haka ya halatta  a fara yin rak'atayil fajr kafin sallar asuba idan an rasa jam'in asuba koda rana ta fito ne.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments