𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Malam dan Allah ina so a min bayani ne a kan raka'atainil fajir. Da wani lokaci ake yin ta. Ana ba da sallar Asuba ce ko yaya? Ina son qarin bayani sosai malam. Mu wuni lafiya, na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam. Raka'atal
Fajri sallah ce mai raka'o'i guda biyu da ake yi bayan Alfijir ya keto, wato
yayin da lokacin sallar Asubahi ya shiga.
Raka'atal Fajri Sunnah ce ba
farilla ba. Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya faɗi falalarta a hadisin Nana A'isha Allah ya
qara mata yarda, wanda Imamu Muslim ya ruwaito, a hadisi mai lamba 725, inda
Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yake cewa
ركعتا الفجر خير من الدنيا وما فيها.
Raka'o'i biyu na sallar Alfijir
sun fi duniya da abin da ke cikinta.
Sannan kuma ba a yin Raka'atal
Fajri sai bayan ketowar Alfijir, kafin a yi sallar Asubahi, kuma sallah ce da
ake taqaita karatu a cikinta, wato Annabi Sallallahu alaihi Wasallam bai yin
dogon karatu a cikinta, yana taqaitawa ne.
Haka kuma idan mutum ya saba yin
Raka'atal Fajri kullum, sai wata rana barci ya rinjeye shi ba laifi ya rama ta
bayan ya idar da sallar Asubahi ko da gari ya yi haske, Saboda an yi hakan a
gaban Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam bai hana ba.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.