𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, malam ina da wata tambaya shin menene hukuncin yin bacci bayan sallar asuba? Allah ya taimaki malam!
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi
Wabarkatahu
To malam babu wani hadisi mai
inganci wanda ya hana bacci bayan sallar asuba, sai dai bayan sallar asuba
lokaci ne mai albarka, wannan yasa Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) idan ya
yi sallar asuba baya tashi daga wurin sallar sai rana ta fito, haka ma
sahabbansa Allah ya yarda da su, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai
lamaba ta: 670. Kuma Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) yana cewa: “Allah ka
sanyawa al’umata albarka a cikin jijjifinta” Tirmizi a hadisi mai lamba ta:
1212, kuma ya kyautata shi. Wannan yake nuna cewa lokaci ne mai albarka, wanda
bai dace da bacci ba, wannan ya sa ko da rundunar yaki Annabi (Sallallahu
alaihi Wasallam) yake so ya aika, yakan aikata ne a farkon yini saboda albarkar
lokacin.
Wasu daga cikin magabata, sun
karhanta yin baccin bayan sallar asuba, Urwatu dan Zubair yana cewa: “Idan aka
ce min wane yana baccin safe na kan guje shi’ kamar yadda Ibnu Abi-shaiba ya
ambata a Musannaf dinsa 5\222. Ya kamata ka shagala da neman ilimi ko kosuwanci
a irin wannan lokacin.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu zarewa
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.