Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halatta A Jingina Dan Zina Ga Ubansa?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘��

Assalamu alaikum Malam Mutum ne yayi zina da Mace har tasamu ciki, kuma ya ce ya yarda yakarbi cikin idan ta haihu yanason ɗansa, Shin a Shari'ance yana halatta ajingina wannan ɗan zinar zuwaga Ubansa na zinar tunda yakarba kokuma a'a bai halattaba??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahamtullahi Wabarkatuh

Mālamai sun ƙārawa jūna sani dangane da hukuncin jingina Ɗan-Zina zuwaga ubansa, dafarkodai dukkan Mālamai sunyi Ittifāƙi akan cewa idan Mutum yayi zina da Mātar aure to ana jingina ɗantane zuwaga mijinta bawai wanda yayi zinar da'itaba, koda kuwa wanda yayi zinar da'ita tasamu cikin yayi da'awar cewa cikinsane, to baza'ayi aiki da maganarsaba matukar dai tahaifi yaron acikin watanni shida ko sama dahaka bayan aure, to za'a jingina wannan ɗan zuwaga mijinta, saidai idan mijinne yakore ɗan ta hanyar Li'āni a kotu.

Sannan idan yakasance Mātar bata da aure kuma wanda yayi mata cikin bai yarda cewa nasa bane, kokuma yaƙi yarda yakarbeshi amatsayin ɗansa, to ananma Ƙaulan-Wāhidan Malamai sukace baza'a jingina wannan Ɗan-Zinar zuwaga wanda yayi mata cikinba,

Amma idan wanda yayi mata cikin yayarda cewa shine yayi, kuma ya yarda yakarɓi cikin amatsayin ɗansa, to anan sai Mālamai sukayi Sāɓānī, mafi yawa daga cikin Mālamai cikinsu harda gālibin Malaman dake Mazhabobinnan guda hudu, duk suntafine akan cewa baza'a riskar da Ɗan-Zina zuwaga ubansa ba koda kuwa uban yakarɓi cikin ya yarda cewa Ɗansane, sukace baza'a jinginashi zuwa gareshiba, daga cikin Dalilansu sunkafa Hujja da wannan Hadisin da Annαвi( ) Ya ce

ﺍﻟﻮﻟﺪ ﻟﻠﻔﺮﺍﺵ ﻭﻟﻠﻌﺎﻫﺮ ﺍﻟﺤﺠﺮ ،

MA'ANA

Ɗa namai-Shinfiɗane (mijinta ko shugabanta idan baiwace) shikuma wanda yayi zina sai ayimasa Hajaru (idan ansamu shaidu kuma yataɓa aure)

Malaman dasuke kan wannan fahimta awajensu baza'a jingina Ɗan-Zina zuwaga ubansaba, hakanan babu gādo tsakanin Ɗan da Uban saidai yagāji uwarsa kawai.

To Saidai kuma agefe ɗaya akwai Mālaman da suka tafi akan cewa ana iya jingina Ɗan-Zina zuwaga ubansa matuƙar dai uban yayi da'awar cewa nasane kuma yakarɓa, Malamai da yawa kamar irin su Ibn-Taymiyya, Ibnul-Ƙayyum, Hasanul-Basariy da wasunsu suna ganin hakan babu laifi musamman idan ya kasance akwai wata Maslaha ta rayuwa da aka kalla, shiyasa ma sukace ya halatta adauramusu aure bayan yayi mata cikin, daga cikin Dalilan Malaman dake kan wannan ra'ayi sunkafa Hujja dacewa asali an halicci wannan yarone da ruwan maniyyin wanda yayi zinar da'ita, kuma ya yarda cewa nasane, sannan sukace ai wancan Hadisin da Annαвi( ) Ya ce

ﺍﻟﻮﻟﺪ ﻟﻠﻔﺮﺍﺵ ﻭﻟﻠﻌﺎﻫﺮ ﺍﻟﺤﺠﺮ ،

Yana magane akan idan mace tanada mijine kaɗai, amma idan bata da miji to Zāhirin Hadisin baya nuna cewa idan mutum ya yarda cewa ɗansane kada ajingina masa shiba, danhaka sukace indai har mutum yāyi iƙirārin cewa ɗansane to za'a jinginashi zuwa gareshi sannan kuma akwai gādo atsakaninsu

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments