𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Malam Wai yaron da aka same shi ba ta
hanyar auren Sunnah ba zai iya gadon iyayensa ko ba zai iya ba a musulunce?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
Al-Imaam At-Tirmiziy da Al-Imaam Ibn Maajah sun riwaito daga
hadisin Amr Bn Shu’aib, daga babansa, daga kakansa cewa: Manzon Allaah (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce
« أَيُّمَا
رَجُلٍ عَاهَرَ بِحُرَّةٍ أَوْ أَمَةٍ فَالْوَلَدُ وَلَدُ زِنَا لاَ يَرِثُ وَلاَ يُورَثُ
»
Duk mutumin da ya yi zina da wata ’ya ko baiwa, to ɗan ɗan zina ne: Ba ya gado
kuma ba a gadon sa. (Sahih Ibn Maajah: 2217)
Al-Imaam At-Tirmiziy ya ce:
وَالْعَمَلُ
عَلَى هَذَا عِنْدَ أَهْلِ الْعِلْمِ أَنَّ وَلَدَ الزِّنَا لاَ يَرِثُ مِنْ أَبِيهِ.
Kuma malamai a kan wannan hadisin ne suke aiki cewa: Ɗan
zina ba ya yin gado daga mahaifinsa.
Sannan kuma malamai sun yi ijma’i a kan cewa: Ɗan
da iyayensa suka yi li’aani
a kansa ko suka same shi ta hanyar zina ba ya gadon wanda ya yi cikinsa, haka
ma danginsa. Shi ma kuma ba zai gaje su ba. Mahaifiyarsa ce kawai ta ke gadon
irin wannan ɗan na
zina ko na li’aani, haka ma danginta. Shi ma kuma yana dagon su.
(At-Ta’aleeqaatur Radiyyah: 3/420).
Amma idan wanda ya yi cikin ya yarda cewa zai riƙe
shi a matsayin ɗansa
da ya samu ta hanyar zina, a nan wasu malamai suna ganin wannan ya mayar da shi
kamar ɗansa na
halal, kuma zai iya gadonsa! Musamman dayake ba shi ɗan ne ya zama sanadin zuwansa duniya ta
wannan mummunar hanyar ba. Laifin iyayensa ne.
Sai dai kuma yarda da wannan maganar tana ɗauke da waɗansu matsalolin da suke
buƙatar
a warware su, kamar haka
1. Shin ɗaukar
wannan matsayin bai ci karo da wannan hadisin sahihi ba, da kuma maganganun
malamai kamar yadda ya gabata a sama ba?
2. Da menene za a iya bambanta wannan ɗan na zina da wanda
iyayensa suka same shi ta hanyar sahihin auren Sunnah kenan?
3. Kuma wannan bai zama kamar taimakawa ne a fakaice ga
cigaba da samar da ’ya’ya ta wannan hanyar da ta saɓa wa Shari’a ba?
4. In kuwa ya zama haka, to da menene za a iya bambanta
wannan da hanyar samun ’ya’ya ta auren mutu’a da ’yan shi’a suke yi?
5. Idan kuma mutane suka yarda da samun haihuwa ta wannan
hanyar abin ba zai kai ga lalacewar gidajen aure ba kenan, kamar yadda abin
yake faruwa a ƙasashen Turai da Amirka?
6. Sannan ko mutane za ta iya jure wa masifu da bala’o’in da
hakan zai iya janyowa musamman a cikin wannan halin na ƙuncin rayuwa da ake
ciki a yau?
7. Amincewa da wannan ɗan
a cikin gida da ɗaukarsa
daidai da sauran ’ya’yan Sunnah, wannan ba zai kai ga cutar da haƙƙoƙin
sauran ’ya’yan ba, kamar a wurin rabon
gado?
Don haka abin da ya fi daidai daga waɗannan bayanan, gara a nisanci bai wa irin
wannan ɗan na zina
matsayi irin na ɗan
Sunnah, har a lokacin da wanda ya yi cikinsa ya amince da shi a matsayin ɗansa. Allaah ya kyauta.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.