Ticker

6/recent/ticker-posts

Mafarkin Yin Lesbian

TAMBAYA (76)

Assalamualaika. Dan Allah malan inadantambaya. Akan mafarkin yin lesbian. Ngd

AMSA

Waalaikumussalam, warahmatullahi, wabarakatuhum

Alhamdulillah

Tabi'i kuma malaminnan na fassarar mafarki Imam Muhammad Ibn Seerin (Rahimahullah) ya ce: Idan mace tayi mafarkin tana madigo da macen da ta sani hakan na nufin zata sanar da ita sirrinta, zata zamo qawarta, zata dinga kwaikwayon halayenta, zata dinga neman shawararta

Idan bata gane wadda take madigo da ita din ba kuma hakan na nufin zata nutse a cikin aikata zunubi. Idan matar aure tayi mafarkin tana madigo da wata matar hakan na nufin mijinta zai sake ta ko kuma zata zama bazawara. Aikata lalata da gawa na nufin namiji ne ko mace na nufin mutuwar mutum idan ya zamana tafiya zakayi to hakan na nufin ziyartar kasar da aka binne mamacin da kayi mafarkinsa/ta

Fassarar kowanne irin mafarkin da ya zama silar zubar maniyyi da zai wajabta wankan janaba na nufin mafarki mara kyau ko kuma saduwa ta baya ko kuma mafarkin saduwa. Yin mafarkin saduwa na iya zama sauke nauyin bashi ko kuma samun waraka daga wata musiba

Idan mace tayi mafarkin tana niqa saffron hakan na nufin ita yar lesbian ce

SHARHI

Idan kinsan kina mu'amala da kawayen banza to ki gaggauta nesantarsu sannan ki canza kawaye na gari domin kuwa zaki iya dabi'antuwa da halinsu wanda karshen al'alamarin shine fadawa fushin Allah idan har baki tuba ba

Sannan ki yawaita addu'ar da Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yake yawan yi; "Ya muqallibil qulub, thabbit qalbi ala dinika" bi ma'ana: "Ya mai jujjuya zuqata, ka tabbatar da ni akan addininka"

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments