Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halatta Amarya Da Ango Su Sanya Zoben Zinari A Ranar Aurensu

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Dan Allah ya halatta Amarya da Ango su sanya zoben zinari a ranar aurensu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahamtullahi Wabarkatuh

Haramun ne ga Namiji yasa zobe ko wani abu na zinari a kowanne irin yanayi. Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya haramta zinare ga mazan wannan al’umma. Yaga wani mutum yana sanye da Zobe na zinare sai shi (Manzon Allah) ya cire zoben daga hannunsa (mutumin) sannan ya ce: Shin ɗayanku zai ɗauki garwashi daga wuta ya rike a hannunsa.

(Muslim ya ruwaito shi, Al-Libaas wal-Zeenah , 3897).

Saboda haka bai halatta ga Namiji yasa Zoben zinari. Amma idan zoben azurfa ne ko sanholama ko wani karfe mai kyalkyali babu laifi Namiji zai iya sanyawa a hannunsa.

Amma ya halatta ga mata suyi amfani da Zoben zinare da kayan da akayi su da zinare.

Saka Zobe tsakanin amarya da ango ko tsakanin Mata da Miji ko tsakanin masoya masu niyyar yin aure, idan an sashi ne da sunan zai kara karfafa soyayyar junansu. To wannan haramun ne qada’an!!!. Saboda ya zama wani nau’in ne na shirka.

(Al-Fataawa al-Jaami’ah lil-Mar’ah al–Muslimah , Mujalladi na 3, shafi na 914-915)

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fb6qgYPXfEeHb8CD1SWAkK

𝐅𝐀𝐂𝐄��𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments