Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sanya Zoben Azurfa Da Zinare

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Menene hukuncin sanya zoben da aka surka azurfa da zinare a cikinsa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Amfani da zoben zinare dai haram ne, saboda hadisai sahihai masu yawa da suka zo a kan hakan. Daga ciki akwai maganarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

« مَنْ كَانَ يُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ فَلاَ يَلْبَسْ حَرِيراً وَلاَ ذَهَباً »

Duk wanda ya kasance yana yin imani da Allaah da Ranar Lahira, to kar ya sanya tufan alharini, haka kuma zinare. (Ahmad: 22248, kuma Al-Arnaa’ut ya ce: Isnadinsa Sahih ne).

Amma idan zoben na azurfa ne, to ya halatta, domin ya tabbata a cikin hadisi cewa: Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ga wani daga cikin sahabbansa sanye da zoben zinare sai ya kau-da-kai daga gare shi. Sai ya yar da shi ya ɗauki zoben baƙin ƙarfe, sai ya ce masa: Ai wannan ya fi sharri, wannan kayan adon yan Wuta ne. Sai ya yar da shi ya ɗauki zoben azurfa. Sai ya yi shiru bai ce masa komai ba. (Ahmad: 6518, kuma Al-Arnaa’ut ya ce: Sahihi ne).

Sannan shi kansa ma ya yi amfani da zoben azurfa, kamar yadda Anas Bn Maalik (Radiyal Laahu Anhu) ya riwaito a cikin Sahih Al-Bukhaariy

اتَّخَذَ خَاتَمًا مِنْ فِضَّةٍ نَقْشُهُ مُحَمَّدٌ رَسُولُ اللَّهِ . كَأَنِّى أَنْظُرُ إِلَى بَيَاضِهِ فِى يَدِهِ .

Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Sallam) ya ɗauki zobe na azurfa, aka karta: Muhammad Manzon Allaah ne a jikinsa. Kamar dai yanzu ga shi ina kallon ƙyallinsa a hannunsa. (Sahih Al-Bukhaariy: 65).

Amma malamai sun yarda idan akwai larura, to ana iya amfani da zinare dan kaɗan. Saboda hadisin Arfajah Bn As’ad (Radiyal Laahu Anhu) wanda aka sare masa hanci a wurin yaƙi, sai ya yi amfani da hanci na azurfa, sai ya riƙa yin wari! Shi ne Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya umurce shi da ya yi amfani da hanci na zinare. (Abu-Daawud: 4232, da At-Tirmiziy: 1770, da An-Nasaaiy: 5161 suka riwaito shi, kuma Al-Albaaniy ya inganta shi).

A kan haka ne malamai suka ce: Ya halatta - ko ma mustahabbi ne - a yi amfani da wani abu kaɗan na zinare a babin larura, kamar a wurin ɗaure haƙora da shi da makamantan hakan.

Amma idan babu irin wannan larurar, to amfanin da zinare yana na a matsayinsa na haramci kome ƙanƙantarsa. Ba za a yi amfani da shi kamar a adon tufafi ba, ko a matsayin warwaro ko igiyar agogo da makamantan hakan ba. (Sahih Fiqhis Sunnah: 3/26).

A ƙarƙashin wannan bayanin, ban ga halaccin yin amfani da zoben da aka surka zinare da azurfa a cikinsa ba, domin ban ga wata larura da za ta halatta yin hakan ba.

Amma fa lallai a gane cewa, wannan hanin da ya zo a cikin waɗannan nassoshin suna magana ne a kan zinare ko azurfar da suke na asali yadda aka sani ne. Ban da inda ake shafa wa ƙarfe ko tasa ko tagulla waɗansu sinadarai a ɗakunan bincike, har kuma su riƙa ƙyalli kamar zinare ko azurfa! Sai a kiyaye da kyau.

Allaah ya ganar da mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments